Sport
Dollar
43,2789
0.22 %Euro
50,2002
-0.1 %Gram Gold
6.375,3800
-0.3 %Quarter Gold
10.664,4800
0.75 %Silver
124,3300
-2.65 %Jami’an ’yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wani mutum mai shekara 30, mai suna Suleman Mamuda, bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a garin Bayawa da ke Karamar Hukumar Augie ta jihar.
Jami’an ’yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wani mutum mai shekara 30, mai suna Suleman Mamuda, bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a garin Bayawa da ke Karamar Hukumar Augie ta jihar.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce ana zargin wanda ake tuhuma da buga wa matarsa da fartanya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.
A cewarsa, Mamuda ya tsere daga yankin bayan faruwar lamarin, amma daga bisani ’yan sanda sun gano inda yake tare da kama shi bayan gudanar da bincike da kuma samun sahihan bayanai daga al’ummar yankin.
“Ya tsere daga yankin bayan faruwar lamarin, amma an gano inda yake tare da kama shi sakamakon binciken ’yan sanda da bayanan da aka samu daga al’ummar yankin,” in ji shi.
SP Usman ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Umar Mohammed Hadejia, ya bayar da umarnin mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da wanda ake tuhuma.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani lamari cikin gaggawa tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.
Comments
No comments Yet
Comment