Sport
Dollar
41,0438
0.01 %Euro
48,1682
0.73 %Gram Gold
4.509,1400
0.59 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Masu garkuwa da mutane a Nijeriya sun buƙaci zunzuruntun kuɗi har Naira biliyan 48 a matsayin kuɗin fansa amma sun samu Naira biliyan 2.57 (kimanin dala miliyan 1.66) a cikin shekara ɗaya, a cewar rahoton kamfanin tsaro na SBM.
Aƙalla mutane 4,722 ne aka yi garkuwa da su a wurare 997 a faɗin Nijeriya tsakanin watan Yulin 2024 zuwa Yuni 2025, yayin da aka kashe mutum 762 a hare-hare da ke da alaƙa da hakan, a cewar wani sabon rahoto da kamfanin tsaro na SBM Intelligence ya fitar a ranar Laraba.
Rahoton, wanda aka yi wa take da “The Economics of Nigeria’s Kidnapping Industry”, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun buƙaci zunzuruntun kuɗi har Naira biliyan 48 a matsayin kuɗin fansa amma sun samu Naira biliyan 2.57 (kimanin dala miliyan 1.66) a cikin shekara ɗaya.
Duk da cewa akwai giɓi mai yawa tsakanin neman kuɗin fansa da kuma samun kuɗi na halak, rahoton SBM ya bayyana cewa kuɗaɗen fansa sun mayar da ƙungiyoyin ta’addanci zuwa ga masu iko, inda suke amfani da kuɗaɗen da suke samu wajen mallakar makamai, da ƙara dabaru, da kuma ɗaukar ma'aikata.
Yankuna da aka fi garkuwa da mutane
Yankin Arewa-maso-Yamma a Nijeriya ne lamarin ya fi shafa, inda aka samu rahoton wurare 425 (42.6%) da kuma mutane 2,938 (62.2%) da aka yi garkuwa da su.
Jihar Zamfara ce ke kan gaba da mutane 1,203, sai Kaduna da kuma Jihar Katsina.
Saɓanin wannan adadin, rahoton SBM ya ce yankin Kudu-maso-Yammacin ƙasar na da kaso mafi ƙanƙanta na aika-aikar masu garkuwa da mutane, inda aka samu kashi 5.3 cikin 100 da kuma kashi 3 cikin 100 na waɗanda abin ya shafa.
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa mafi yawan sace-sacen jama'a da ake yi ko kuma garkuwa da mutum fiye da biyar na faruwa ne galibi daga yankin Arewa.
Comments
No comments Yet
Comment