Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 202. An kashe aƙalla Falasɗinawa 34,262 - galibinsu jarirai da yara da mata. An jikkata sama da 77,229. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗaya a G

'Yan Houthi na Yaman sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila da Amurka da Birtaniya 102 a rikicin Gaza

1558 GMT — 'Yan Houthi na Yaman sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila da Amurka da Birtaniya 102 a rikicin Gaza

'Yan Houthi na Yaman sun ce sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila da Amurka da Birtaniya 102 tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza a watan Oktoban da ya gabata.

Shugaban kungiyar Abdul Malik al Houthi ya ce, an kai wa wasu jiragen ruwa na Isra'ila da Amurka da Birtaniya hari a cikin kwanaki 202 na hare-haren wuce gona da iri kan Gaza.

Ya ce kusan jiragen ruwa biyu masu alaka da Isra'ila ne dakarun Houthi ke kai wa hari a kullum.

Ya kara da cewa, "Yawan zirga-zirgar jiragen ruwa na Amurka a cikin Tekun Maliya ya ragu da kashi 80 cikin 100."

1639 GMT — Yunwa na ƙara kunno kai a arewacin Gaza, ana buƙatar ƙarin agaji - Jami'in WFP

Arewacin Gaza na ci gaba da fuskantar yunwa da buƙatar kayan agaji mai yawa, da karin hasashen samun damar shiga da kuma ci gaba da kokarin samun karin taimako iri-iri a yankin, in ji mataimakin babban daraktan hukumar samar da abinci ta MDD (WFP) Carl Skau.

1312 GMT — Kasashe 18 sun yi kira ga Hamas da ta saki wadanda take garkuwa da su domin tsagaita wuta

Shugabannin kasashe 18 da ake ci gaba da garkuwa da 'yan kasarsu a Gaza da aka yi wa ƙawanya, sun buƙaci a sake su cikin gaggawa tare da cewa hakan zai kai ga abin da suka kira "sahihancin kawo karshen tashin hankali."

Sanarwar da shugabannin kasashen Ajantina da Austria da Brazil da Bulgaria da Canada da Colombia da Denmark da Faransa da Jamus da Hungary da Poland da Portugal da Romania da Serbia da Spain da Thailand da Birtaniya da kuma Amurka suka fitar ta ce makomar wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza, "wadanda ke da kariya a karkashin dokokin kasa da kasa, abin damuwa ne sosai da al'ummar duniya."

"Muna jaddada cewa yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da take kan teburin tattaunawa, za ta sa a tsagaita wuta a Zirin Gaza, lamarin da zai sauƙaƙa ƙarin taimakon jinƙai da za a kai a duk fadin Gaza, da kuma kai ga kawo karshen tashin hankali," ya ce.

1411 GMT — Hamas ta matsa wa Isra'ila lamba da ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza idan tana so ta saki mutanen da take garkuwa da su

Hamas ta sake jaddada bukatar Isra'ila ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza a matsayin wani bangare na duk wata yarjejeniya ta sako mutanen da aka yi garkuwa da su a can, kamar yadda Sami Abu Zuhri, wani babban jami'i a kungiyar ta gwagwarmayar Falasdinu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, yana mai cewa matsin lambar da Amurka ke yi wa Hamas ba shi da wani amfani.

0940 GMT — Yawan waɗanda suka mutu a Gaza ya kai 34,300 yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare

Yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-hare ba ƙaƙƙautawa da Isra'ila take kai wa Gaza tun watan Oktoban bara sun kai 34,305, kamar yadda Ma'aikatar lafiya ta yankin da aka yi wa ƙawanya ta faɗa.

Wata sanarwa ta ma'aikatar ta ce an kuma raunata mutum 77,293 tun fara yaƙin.

Falasdinawan suna jimamin 'yan'uwansu da aka kashe a harin bam da Isra'ila ta kai a asibitin al-Najjar da ke Rafah a kudancin Gaza, a ranar 25 ga Afrilu, 2024 a ci gaba da hare-haren Isra'ila kan yankin da ke kewaye. / Hoto: AFP

"Aƙalla mutum 43 aka kashe tare jikkata wasu 64 a hare-haren da Isra'ila ta kai cikin awa 24 da suka wuce," in ji ma'aikatar.

"Mutane da dama sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai a kan tituna a yayin da masu aikin ceto suka kasa kaiwa gare su," ta ƙara da cewa.

0550 GMT — Hamas za ta ajiye makamanta idan aka kafa ƙasashe biyu masu ƴancin kansu: Rahoto

Wani babban jami'i a ɓangare siyasa na Hamas ya shaida wa The Associated Press cewa a shirye ƙungiyar take ta ƙulla yarjejeniyar shekara biyar ko fiye da haka da Isra'ila kuma za ta zama jam'iyyar siyasa idan aka samar da ƙasashe biyu kowace mai cin gashin kanta.

Al-Hayya ya ce Hamas tana son kafa gwamnatin haɗin-kai a Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan./Hoto: AFP

Khalil al-Hayya ya bayyana haka ne ranar Laraba a yayin da aka fuskanci tsaiko kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

Al-Hayya ya ce Hamas tana son kafa gwamnatin haɗin-kai a Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Ya ƙara da cewa Hamas za ta amince “da cikakkiyar ƙasar Falasɗinawa da ke da iko a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gaza da kuma mayar da Falasɗinawa yankin kamar yadda dokokin ƙasashen suka buƙaci a yi".

0201 GMT — An fitar da Ben-Gvir daga wajen da Isra'ilawa masu zanga-zanga suka yi wa ƙawanya

'Yan sandan Isra'ila sun fitar da minista mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir daga wani gini da ke Yammacin Birnin Ƙudus wanda masu zanga-zanga suka kewaye, ciki har da iyalan waɗanda ake garkuwa da su a Gaza.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, daruruwan masu zanga-zangar ne suka taru a yankin da ke kusa da ginin inda ministan kula da kayayyakin tarihi na kasar Amchai Eliyahu na masu tsattsauran ra'ayi da malamin addinin Kirista Bentzi Gopstein suka raka Ben-Gvir.

Rundunar ‘yan sandan ta fitar da fitaccen ministan daga wajen da lamarin ya faru bayan jami’anta sun cece shi.

Sun hana masu zanga-zangar isa ga Ben-Gvir ne bayan sun kewaye motarsa ​​suna rera taken rashin amincewa da shi da suka hada da "Shame on you," wato "Ka ji kunya."

'Yan sandan sun yi amfani da hanyoyin tarwatsa jama'a, ciki har da watsa wa mutane ruwan datti, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Rundunar ‘yan sandan ta fitar da fitaccen ministan daga wajen da lamarin ya faru bayan jami’anta sun cece shi. / Photo: Reuters
#