Sport
Netanyahu, wanda yake son Amurka ta ƙara matsin lamba kan Iran, an shigar da shi fadar White House ta wata hanya ta gefe ba tare da samu faretin ban-girma daga dogaran fadar kamar yadda aka saba ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba a cim ma wani takamaiman abu ba yayin ganawarsa "mai matuƙar kyau" da Firaministan Isra'ila Isra’ila Benjamin Netanyahu amma za a ci gaba da tattaunawa da Iran da zummar ƙulla wata yarjejeniya.
"Babu wani takamaiman abun da aka cim ma fiye da cewa na nanata cewa a ci gaba da tattaunawa da Iran domin ganin ko za a iya ƙulla yarjejeniya ko kuma a’a," kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social bayan ya gana da Netanyahu a Fadar White House.
"Idan hakan zai yiwu, na shaida wa Firaministan cewa wannan ne abin da zan fi so. Idan ba zai yiwu ba, dole mu kalli yadda sakamakon zai kasance," in ji Trump, yana mai ƙarawa da tuni game da hare-haren da Amurka ta ƙaddamar kan tashoshin nukiliyar Iran a shekarar da ta gabata.
"Bugu da ƙari, mun tattauna kan gagarumin ci-gaban da ake samu a Gaza, da ma yankin baki ɗaya ."
Ofishin Netanyahu ya ce a lokacin tattaunawar da Trump Firaministan na Isra’ila ya "nace kan tsaron Isra’ila game da tattaunawa" da Iran.
Ganawar ta bakwai tsakanin mutanen biyu tun bayan Trump ya koma karagar mulki an yi ta ne a ɓoye, inda Netanyahu ya sulale ta wata hanya ta gefe ba tare da ya karɓi faretin ban-girma da dogaran fadar suka saba yi wa baƙi ba.
Netanyahu ya gana da Trump ne domin ya sa a ƙara matsin lamba a tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, inda ake zaman ɗarɗar a yankin Gabas ta Tsakiya game da barazanar harin sojin Amurka.
An ga Trump da Netanyahu suna tafawa a wani hoton da ofishin Firaministan Isra’ila ya fitar yayin da aka hana manema labarai shiga wajen ganawar.
Washington da Tehran sun sake soma tattaunawar nukiliya a makon jiya a Oman.
An dakatar da tattaunawar bayan Amurka ta ƙaddamar da hare-haren sama kan tashoshin nukiliyar Iran yayin yaƙin kwanaki 12 da ta yi da Iran a watan Yulin da ya gabata.
Comments
No comments Yet
Comment