Sport
Dollar
42,9820
0.01 %Euro
50,7625
-0.15 %Gram Gold
5.965,9500
0 %Quarter Gold
10.158,3200
0 %Silver
98,9300
0 %'Idan Israʼila ta yi amfani da yankin ta kai wa wasu hari, su ma waɗannan za su kai wa Somaliland da Somalia hari,' kamar yadda Shugaban Somalia ya yi gargaɗi bayan Tel Aviv ta amince da yankin da ya ɓalle.
Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya ce ƙasarsa ba ta son Isra'ila ta samu gindin zama a Somaliland, yana mai gargadin cewa amincewar Tel Aviv da yankin da ya ke neman fita daga Somaliya na iya kawo rikice-rikicenta zuwa yankin.
‘Ba mu taɓa kai hari kan Isra'ila ba. Ba mu taɓa haifar wa Isra'ila wata matsala ba. Ba ma so Isra'ila ta zo wurinmu ta kawo mana matsalarta,’ Mohamud ya shaida wa gidan kafar watsa labarai ta ƙasar Turkiya TRT World a wata hira ta musamman.
Ya bayyana wannan matakin a matsayin 'halin baƙin ciki sosai,' yana kiran a girmama dokokin ƙasa da ƙasa.
Mohamud ya ce ayyukan baya-bayan nan na Isra'ila ba su dace da dokokin ƙasa da ƙasa ba, inda ya nuna misalai daga Gaza da dogon tarihi na rikice-rikice a Gabas Ta Tsakiya.
‘Abin baƙin ciki ne sosai cewa yanzu an mayar da hakan zuwa Somaliya,’ in ji shi.
Goyon bayan duniya
Mohamud ya ce Mogadishu ta tuntuɓi al'ummar duniya, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka, Hukumar Shirin Bunƙasa Ƙasashe (IGAD), Ƙungiyar Ƙasashen Gabashin Afirka (EAC), Kungiyar Larabawa da Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai (OIC), waɗanda suka goyi bayan Somaliya, kuma a fili suka tabbatar da goyon bayansu ga 'yancin ƙasa da haɗina kan ƙasar.
Ya ce yankunan arewacin Somaliya ya daɗe yana fuskantar yunƙurin ɓallewa, amma a kullum gwamnati ta na ƙoƙarin warware bambance-bambancen cikin lumana.
‘Gwamnatin Somaliya ba ta taɓa ƙoƙarin tilasta wa, ko yaƙi, ko amfani da ƙarfi na diflomasiyya kan waɗannan mutanen ba,’ in ji shi.
Mohamud ya ce Turkiyya ta yi ƙoƙarin yin sulhu tsakanin Somaliland da Somaliya, tare da gudanar da taruka a shekarar 2015 da kuma wanzar da wakili a Hargeisa don ci gaba da tattaunawa.
Ankara tana da tarihin kasancewa tare da Somaliya, in ji Mohamud, kuma tana goyon bayan haɗin kai da 'yancin ƙasar a lokutan ƙalubale.
Ya ƙara da cewa Turkiyya na da al'adar 'ko da yaushe' tana kasancewa tare da mutanen da aka yi musu rashin adalci.
Amincewa na iya ƙara tashin hankali
Mohamud ya ce Somaliya na samun goyon bayan al'ummar duniya duk da amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland.
Shugaban Somaliya ya ce batun yana da matuƙar muhimmanci duba da ayyukan baya-bayan nan na Isra'ila a Gabas Ta Tsakiya, ba kawai a kan Falasdinu ba har ma a Siriya da Lebanon, wanda ya haifar da damuwa game da shiga harkokinta a Tekun Maliya, da Gabar Teken Adan, da Kusurwar Afirka, wanda ya kira 'yanki mai fuskantar matuƙar tashin hankali'.
Ya ce kasancewar Isra'ila a wajen na iya haifar da sabon rikici a wasu sassan Somaliya da ƙasashen makwabta masu daura da Gaɓar Tekun Adan da Tekun Fasha na Larabawa, yana nuna cewa Houthi ta Yemen da Iran ma suna da dangantaka mai muni da Isra'ila.
'Idan Israʼila ta yi amfani da yankin ta kai wa wasu hari, su ma waɗannan za su kai wa Somaliland da Somalia hari,' kamar yadda Shugaban Somalia ya yi gargaɗi bayan Tel Aviv ta amince da yankin da ya ɓalle,’ in ji Mohamud a gargaɗin da ya yi.
Ya ce kafa sansanin soja a Somaliland da tilasta wa Falasdinawa yin ƙaura zuwa yankin zai ƙara dagula rikicin, abin da gwamnati da al'ummar Somaliya suka yi watsi da shi gaba ɗaya.
Tun da farko, Mohamud ya shaida wa tashar labarai ta Qatar, Al Jazeera cewa, Somaliland ta amince za ta tsugunar da Falasdinawa, za ta karɓi sansanin soja na Isra'ila, kuma ta shiga Yarjeneniya Abraham, inda ita kuma Isra’ila za ta amince da Somaliland a matsayin kasa mai son gashin kanta, yana mai ambato rahotannin leken asiri.
Haɗin gwiwar Somaliya da Turkiyya
Shugaban na Somaliya ya jaddada haɗin gwiwa masu ma’ana da Turkiyya, yana nuna cewa haɗin gwiwar tasu ya haɗa da fannonin tsaro, diflomasiyya, zuba jari, albarkatun ƙasa, harkokin teku, — tattalin arzikin teku.
Ya ce kwanan nan ya yi wa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan cikakken bayani kan cigaban Somaliya a fannin tsaro, dimukradiyya, da gina ƙasa, kuma sun tattauna yadda za a hanzarta ayyukan haɗin gwiwa.
Mohamud ya ce zuba jai kai-tsaye daga ƙasashen waje 'tabbas' zai shigo Somaliya.
Comments
No comments Yet
Comment