Sport
Dollar
42,1216
0.07 %Euro
48,6499
0.52 %Gram Gold
5.434,8000
0.79 %Quarter Gold
9.147,6900
1.02 %Silver
65,9900
1.27 %Tottenham ta fitar da sanarwa kan ɗan wasanta, Destiny Udogie, wanda aka yi wa barazana da bindiga.
Gabanin wasan maraicen Talatar nan da Tottenham da lallasa Copenhagen da ci 4-1, wasu rahotanni sun fito a Italiya suna bayyana cewa wani ɗan wasan ƙasar ya samu barazana daga agent ɗinsa.
Rahotannin na cewa lamarin ya faru ne tun a Satumba a wani layi a birnin London, kuma ɗan wasan da abin ya rutsa da shi, Destiny Udogie, yana buga wa Tottenham da tawagar Italiya wasa.
Tottenham ta fitar da sanarwa game tana cewa: "Muna bai wa Destiny da iyalansa ƙwarin gwiwa tun bayan faruwar lamarin. Ganin batu ne na shari’a, ba za mu ba da ƙarin bayani ba."
Wasu bayanai na cewa lamarin ya zo daidai da lokacin da Udogie ya sauya agent ɗinsa, inda ya koma kamfanin agent mai suna Elite Project Group.
Sabon kamfanin agent ɗin shi ne ke wakiltar shahararrun ‘yan wasa kamar Bukayo Saka, Jamie Gittens, Jadon Sancho, Romeo Lavia, Alex Iwobi, da ma wasu ƙari.
An bayyana cewa Udogie ya yi sauyin ne don ya samu sabuwar kwantiragi da Spurs, amma ba a ambaci ko batun na da alaƙa da lamarin barazana da aka masa da bindiga ba.
Tarihin Udogie a Tottenham
Destiny Udogie ya zo Spurs ne daga Udinese a 2022, inda da fari ya ci gaba da zama a ƙungiyar da ke Italiya kafin ka koma Ingila.
Zuwa yanzu, ya buga wasanni 75 a Spurs ƙarƙashin tsohon koci, Ange Postecoglou, da kuma a yanzu ƙarƙashin sabon koci Thomas Frank.
Ita ma hukumar ‘yan sandan London, Metropolitan ta sanar cewa, "An kira ‘yan sanda da ƙarfe 23.14 na Asabar, 6 ga Satumba, aka kawo rahoton wani mutum da ya haura shekara 20, an yi masa barazana da bindiga.”
“Jami’anmu sun yi magana da wanda abin ya shafa kuma yayin bincikensu, sun ji cewa wani mutumi mai sama da shekara 20 an yi masa barazana, amma babu rahoton jin ciwo a duka lamarin,” in ji sanarwar.
Daga ƙarshe sanarwar ta ce, “An kama wani mai shekara 31 ranar Litinin, 8 ga Satumba kan zargin mallakar bindiga da niyyar tursasawa, da kuma yin tuƙi ba tare da lasisi ba. An yi belin sa yayin da ake ci gaba da bincike."
Comments
No comments Yet
Comment