Sport
Dollar
41,1828
0.23 %Euro
48,1704
-0.04 %Gram Gold
4.563,1300
1.19 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Jaririn goggon birin da aka yi fasa-kwaurinsa aka kuma gano shi a filin jirgin sama na Istanbul, na shirin komawa gida Nijeriya, bayan ba shi kulawa a Istanbul ya kuma murmure, kamar yadda hukumomin Turkiyya suka bayyana.
Jaririn goggon birin da aka saka wa suna "Zeytin", wanda aka gano a filin jirgin sama na Istanbul, a kan hanyarsa zuwa Thailand daga Nijeriya a 2024, na shirin komawa Nijeriya bayan an yi jinyarsa ya kuma farfado a gidan kula da namun daji da ke Polonezköy, Turkiyya.
Babban daraktan Hukumar Raya Gandun Daji na Turkiyya (DKMP) Kadir Çokçetin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an gano Zeytin ne a filin jirgin saman Istanbul a kan hanyarsa ta zuwa Thailand daga Najeriya, a watan Disambar 2004.
Çokçetin ya bayyana cewa Zeytin ya shiga ran jama'a ba kawai a Turkiyya ba, har ma da duniya baki daya, inda ya ce ana sa ido sosai a kansa a duniya, musamman ma Majalisar Dinkin Duniya da Sakatariyar Yarjejeniyar Kasa da Kasa kan Nau'o'in Dabbobin daji da ke fuskantar barazanar bacewa (CITES).
Çokcetin ya bayyana cewa bayan bincike, kungiyoyi sun kwace jaririn goggon birin, saboda wadanda suke dauke da shi ba su da takardun CITES.
Ya ce an kula da Zeytin kuma an duba shi a cikin yanayi mai kyau da ba shi kariya. "Lokacin da aka same shi, yana cikin firgici sosai, ya gaji, yanzu kuma kamar yadda kuke gani, ya murmure, ya yi kyau sosai, ya fara buga kirjinsa, yana kokawa da masu tsaronsa," a cewar Çokcetin.
‘Zeytin na shirin komawa Nijeriya’
Comments
No comments Yet
Comment