Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 84 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 21,320, sannan sun jikkata fiye da mutum 55,603, a yayin da kasar ke ci gaba da luguden wuta a yankunan Falasdinawa.

Yawan Falasdinawan da aka kashe a hare-haren Isra'ila sun kai 21,500 — Ma'aikatar Lafiya ta Gaza

1323 GMT Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 300 a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya tun ranar 7 ga Oktoba

Rundunar sojin Isra'ila ta kashe jimillar Falasdinawa 308 da ke samun mafaka a cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda hukumar ba da agaji ta MDD mai kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu a yankin Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ya fada.

“Rahotanni na farko sun nuna a ranar 25 ga watan Disamba, cewa an kashe mutum biyu 2 da ke mafaka a makarantar Maghazi Prep ta UNRWA, yayin da daya ya samu raunuka, sakamakon harin da aka kai kai tsaye,” in ji hukumar a cikin wata sanarwa.

Hukumar ta ƙara da cewa, tun bayan da aka fara yaƙin, aƙalla mutum 308 ne suka rasa rayukansu a matsugunan UNRWA, tare da bayyana cewa wasu 1,095 sun jikkata.

Hukumar ta jaddada cewa "babu wani wuri a Gaza da ke da aminci."

1345 GMT Kungiyar Hizbullah ta kai hari kan sansanonin sojin Isra'ila a kusa da iyakar Lebanon

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta ce ta kai hari kan wuraren da sojojin Isra'ila suke yi a kan iyakar kudancin Lebanon.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta sanar da cewa mayakanta sun kai hari kan wani katafaren jirgin da ke dauke da kayan leken asiri a yankin Dovev.

Har ila yau, Hezbollah ta ce mayaƙanta "sun kai hari kan yankin Hadab Yaron na Isra'ila da makaman da suka dace" tare da samun wajen "kai tsaye."

1156 GMT — Yawan Falasdinawan da aka kashe a hare-haren Isra'ila sun kai 21,500 — Ma'aikatar Lafiya ta Gaza

Aƙalla Falasɗinawa 187 aka kashe a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza a cikin awa 24 da suka wuce, adadin da ya sa yawan waɗanda suka mutu zuwa yanzu ya kai 21,507 tun 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma'aikatar Lafiya da ke yankin da aka yi wa ƙawanya.

Ma'aikatar ta kuma ƙara da cewa mutum 55,915 ne suka jikkata tun bayan yaƙin da Isra'ilan ta fara a yankin.

Tun bayan ɓarkewar mummunan yaƙin Isra'ila a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, fiye da kashi 80 cikin 100 na al'ummar Gaza miliyan 2.4 aka raba da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

0930 GMT — Sojojin Isra'ila sun sanar da fadada hare-harensu a Khan Younis da ke kudancin Gaza

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da fadada ayyukanta na soji a Khan Younis da ke kudancin Gaza.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce: "Sojojin Isra'ila suna fadada kai hare-harensu a yankin Khan Younis."

"Dakarun sun fara kai hari jiya (Alhamis) da yamma domin lalata ababen more rayuwa na abokan gaba a birnin Khan Younis," in ji sanarwar.

0613 GMT — Isra'ila ta bude wuta kan ayarin motocin kayan agaji - UNRWA

Sojojin Isra'ila sun bude wuta a kan ayarin motocin da ke dauke da kayan agaji a yayin da suke komawa daga Arewacin Gaza a kan hanyar da rundunar sojin Isra'ila ta amince a bi, a cewar Hukumar Bayar da Agaji ga Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA.

“Sojojin Isra'ila sun bude wuta a kan ayarin motocin a yayin da suke komawa daga Arewacin Gaza a kan hanyar da sojojin Isra'ila suka yarda a bi,” in ji Thomas White, daraktan Hukumar a Zirin Gaza, a wata sanarwa da ya fitar.

“An jikkata shugabanmu na kasashen duniya da tawagarsa sannan an lalata mota daya,” in ji shi.

White ya jaddada cewa “bai kamata a rika kai hari kan ma'aikata ba.”

2348 GMT — Hamas ta ce kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza yana da muhimmanci

Rundunar sojin kungiyar Hamas ta Falasdinu ta bayyana cewa kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza shi suka fi fifitawa, tare da jaddada yin watsi da duk wata yarjejeniyar musaya ko tattaunawa inda har ba a cika wannan sharadi ba.

An bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da Abu Ubaida, mai magana da yawun rundunar Al Qassam Brigades ya yi, wanda aka watsa a tashar talabijin ta Aljazeera.

Abu Ubaida ya sanar da cewa mayakan Al Qassam "sun lalata motocin soji fiye da 825, da suka hada da manyan motocin yaƙi da tankokin yaƙi tun farkon mamayar da Isra'ila ta kai ta ƙasa."

Ya ƙara da cewa: "Abin da muka sa a gaba shi ne mu dakatar da kai hare-hare kan al'ummarmu a Gaza, kuma babu wani fifiko da ya wuce haka."

Ya jaddada cewa "ba za mu amince da duk wata yarjejeniyar musaya ko shawarwari ba kafin a daina kai hare-hare kan al'ummarmu a Gaza."

Wani yaro da ya jikkata a harin da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat yana samun kulawa a asibitin shahidan Al Aqsa/ Hoto: AA

0128 GMT — Amurka ta yi ikirarin harbo jirgin yaki mara matuki da makami mai linzami da 'yan Houthi suka harba

Wani jirgin ruwan yaƙin Amurka ya harbo wani jirgin yaƙi mara matuƙi da makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi na Yaman suka harba, in ji rundunar sojin Amurka.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta fitar ta ce, jirgin yaƙin USS Mason [DDG 87] ya harbo wani makami mai linzami guda ɗaya a Kudancin Tekun Maliya da Houthis suka harba.

CENTCOM ta ƙara da cewa, babu wata ɓarna da aka samu ko ɗaya daga cikin jiragen ruwa 18 da ke yankin, sannan babu wanda ya samu raunuka, inda ya ƙara da cewa shi ne karo na 22 na yunƙurin kai hari kan jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa da Houthis suka yi tun tsakiyar watan Oktoba.

#