Dollar

43,1388

0.21 %

Euro

50,2459

-0.08 %

Gram Gold

6.246,2500

0.83 %

Quarter Gold

10.381,6000

0.77 %

Silver

110,7700

4.07 %

Sojin Sudan sun ce aikin da suka yi ta sama da ƙasa sun lalale ɗaruruwan motoci a cikin mako guda.

Yaƙin Sudan: Sojojin sun ce sun yi wa sojojin RSF lugude a Darfur da Kordofan

Sojojin Sudan sun ce sun yi wa Rundunar ‘Yan Sa-Kai ta (RSF) mummunar asara mai yawa yayin jerin harare-hare ta sama da ƙasa da aka gudanar a makon da ya gabata a yankunan Darfur da Kordofan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, rundunar ta ce dakarunta sun kai farmaki kan wuraren RSF, sun lalata kimanin motocin yaki 240 kuma sun kashe ɗaruruwan mayaƙa.

Sojojin sun ce harin ya kuma nufi abin da suka bayyana a matsayin wuraren kayan aikin sufuri da ayyukan RSF, ciki har da wuraren da suka shafi jiragen sama marasa matuki da wuraren ajiya, da kuma wurare a Filin Jirgin Sama na Nyala a Kudancin Darfur.

Sun ƙara da cewa dakarun ƙasa kuma sun samu nasarar korar mayaƙan RSF daga yankuna masu yawa a Darfur da Kordofan, kuma ana ci gaba da gudanar da ayyuka domin bin sauran 'yan kungiyar.

RSF ba ta yi martani ba kan bayanin sojojin har yanzu.

Fararen hula masu gudun hijira

A 'yan makonnin da suka gabata, rikici ya ƙaru a jihohin Kordofan uku na Sudan – Arewa, da Yamma da Kudu – inda fafatwar ɓangarorin biyu ta tilasta wa dubu-dubban fararen hula barin gidajensu.

Daga cikin jihohi 18 na Sudan, RSF ce ke iko da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur a yamma, in ban da wasu sassan Arewacin Darfur da har yanzu rundunar soji ke iko da su. A gefe guda kuma, sojoji na riƙe da mafi yawan yankuna a cikin sauran jihohi 13 a kudu da arewa da gabas da tsakiyar ƙasar, ciki har da babban birnin ƙasar Khartoum.

Matsalar jin ƙai a Sudan ta ƙara ta'azzara tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin sojoji da RSF a watan Afrilu 2023 kan saɓani na haɗe rundunar sojan ƙasar ta zama guda ɗaya, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubu-dubatar mutane da kuma ƙaurar milyoyi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#