Dollar

43,0407

0.03 %

Euro

50,3034

-0.3 %

Gram Gold

6.122,2600

2.18 %

Quarter Gold

10.337,8100

0.07 %

Silver

105,6500

5.24 %

Zaman tankiya da aka shefe shekaru biyu ana yi tsaanin Benin da Nijar ya kai ga ƙasashen biyu na Yammacin Afirka masu maƙotan juna ɗaukar matakin ramuwar gayya ta hanyar korar jakadun juna, kamar yadda kasashin biyu suka bayyana ranar Lahadi.

Benin da Nijar suka kori jakadun juna a matakin ramuwar gayya

Bayan shekaru biyu zaman doya da manja na ƙara tsanani tsakanin Benin da Nijar, wannan makon maƙwabtan na Yammacin Afirka sun gudanar da musayar korar jakadun juna, in ji majiyoyin diflomasiyya na ƙasashen a ranar Lahadi.

Hulɗarsu ta kasance ta je-na-yi-ka tun bayan juyin mulkin soji a Nijar da ya kifar da Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.

Nijar na ikirarin cewa Benin na son dagula lamura a cikin ƙasarta, wani zargi da Cotonou ta musanta.

A 'yan kwanakin baya Benin ta kori wani jami'in leƙen asiri da kuma wani jami'in 'yan sanda da ke aiki a ofishin jakadancin Nijar a Cotonou, in ji wata majiya ta diflomasiyyar Benin, wadda ba ta bayyana dalili ba.

A matsayin ramawa, Nijar a cikin wata sanarwa a rana Alhamis ta ayyana wani babban jami’in diflomasiyya a ofishin jakadancin Benin a Niamey a matsayin 'wanda ba a buƙatarsa a kasar' tare da ba shi sa’o’i 48 ya bar ƙasar, tana mai cewa matakin na ramuwar gayya ne ga Cotonou.

Nijar ta yi ƙawance da Burkina Faso da Mali, maƙwabta biyu da suke ƙarkashin mulkin soji. Dukkanin kasashen uku sun fita daga Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda Benin ke cikin ta, inda suka kafa wata ƙungiyar haɗin kai da ake kira Alliance of Sahel States (AES).

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#