Da yawan matasa a Nairobi sun ce talla na tallafa musu su kula da iyalansu.

Yadda talla a kan tituna ke rufa wa matasa asiri a babban birnin Kenya

Daga Dayo Yusuf

Ƙarin matasa a Kenya suna rungumar talla a kan titi, abin da ke nuna halin dogewa da kuma jajircewa.

"Ni ɗan talla ne. Wato mai sayar da kaya kuma ina alfahari da sana'ata," Francis Gachanja ya faɗa yayin da yake ɗaura igiyar takalminsa a gida don fara aikinsa na ranar.

Francis mazaunin Ruiru ne, wani ƙaramin gari a wajen Nairobi. Yana fara ayyukansa na rana ne da shirya ƴaƴansa maza guda biyu domin tafiya makaranta, ya taimaka wa matarsa da ƴan aikace-aikace, sannan tattaro jakunkunansa ya nufi tsakiyar gari don kasuwanci.

Sana'a ce da ya ce yana yi tun da ya kammala makarantar sakandare.

"Tun da na kammala makarantar sakandare sana'a ɗaya tilo da na sani ita ce talla," Francis ya gaya wa TRT Afrika.

"Yi Wa al'umma Hidima"

"Wannan sana'ar ce take ciyar da iyalina, sa'annan take taimaka min na kai ƴaƴana makaranta. Ita ce ke samar min da wata buƙatata a matsayina na miji ko uba," Francis ya bayyana.

Matsayin Francis da iyalinsa da kuma gidansa ya cika shedar cewa sana'ar talla babbar madogara ce a rayuwarsa.

Saboda wannan sana'ar ce har ya iya gina gida kuma ya tura ƴaƴansa makaranta.

Amma bayan gajiyar tattalin arziƙi, Francis na kallon sana'ar tasa a matsayin yi wa al'umma hidima.

"Abokanan hulɗarmu galibinsu masu ƙaramin ƙarfi ne, mutane da samunsu tsakatsaki ne, da kuma waɗanda ba manya attajirai ba ne. Waɗannan su ne suke tallafa mana saboda sauran hamshaƙan, manyan masu kuɗi da masu hannu da shuni a ƙasar nan, yana wahala ka gan su a waɗannan titunan da muke sana'armu," in ji Francis.

Francis ya ce galibin abokan hulɗarsu ƴan tsakatsaki da masu ƙaramin ƙarfi ne. Hoto: TRT Afrika

Duk da wannan sana'ar tana ba shi amfani, amma tana tattare da ƙalubale. Tun farko a wannan watan, gwamnan Nairobi, Johnson Sakaja ya bayar da umurnin kawar da duk ƴan talla daga titunan birnin, yana cewa suna tattare motoci, su jawo cunkoso da kuma gurɓata birnin.

'Ina ƙaunar sana'ata'

"Babu tallan kaya a kan titi. Rataye kaya a kan hanya, babu! Ba za mu ƙyale wannan ba," Sakaja ya ce.

"Wannan abu ne da ya wajaba kuma domin kare lafiyarsu. Ba za mu ƙyale tallace-tallace a kan tituna ba sannan za mu fara aiwatar da dokar nan-take," ya ƙara da cewa.

Amma ba wannan ba ne karon farko da mahukuntan birnin ke sa-in-sa da ƴan talla. Francis ya ce sun yi iya bakin ƙoƙarinsu, su ba wa gwamnati haɗin kai game da waje da lokacin da za su gudanar da kasuwancinsu.

Francis Gachanja ya gina gida da sana'ar talla a kan titi. Hoto: TRT Afrika

Duk da waɗannan ƙalubalen, Francis ya ce su ma mahukuntan na samun kuɗaɗen-shiga daga harkokin nasu.

''Muna biyan hukuma haraji duk da wasu kuɗaɗen ba a tantance ko na mene ne ba. Yanzu suna gina kasuwa inda za a dinga tatsar mu shillings 100 zuwa 200 a kullum."

Alƙaluman hukuma na baya bayan nan sun nuna cewa rashin aikin yi tsakanin matasa a Kenya yana kashi 35.

Francis ya yi kira ga gwamnati da ta inganta ƴan talla ta bujuro da manufofi da suka fi inganci don bunƙasa harkokin kasuwancinsu da kuma samar da ƙarin aikin yi.

Alƙaluman hukuma na baya bayan nan sun nuna cewa rashin aikin yi tsakanin matasa a Kenya yana kashi 35. ne / Hoto : TRT Afrika

"Ina daraja wannan sana'ar duk da ƙalubalen da suke tattare da ita. Idan na ce ba na daraja ta, wane zaɓi nake da shi? A ina zan samu wajen neman abinci? Ko da tana fuskantar ƙalubale masu yawa ne, dole ka so ta," Francis ya kammala.

#