Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun kusa 300, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu.

Yadda ƴan bindiga suka sace ɗalibai kusan 300 a wata makarantar firamare a Kaduna

Rahotanni daga Nijeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun sace gomman ɗalibai na wata makarantar firamare a ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a yau Alhamis.

Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun kusa 300, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu.

TRT Afirka Hausa ta yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumomi na gwamnatin jihar da na jam'ian tsaro, amma ba a same su ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa waɗanda suka shaida lamarin sun ce abin ya faru ne a lokacin da yaran suke halartar taro na asambili, kana daga bisani ƴan bindigan su kora ɗaliban da suka sace ɗin cikin daji.

Ƴan bindiga da ke yawan kai hare-hare sun sha satar ɗalaibai a wasu jihohin arewacin Nijeriya, lamarin da yake yin mummunan tasiri a kan fannin ilimi a ƙasar.

#