Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar wa Fadar White House cewa zai yi magana kai-tsaye da Shugaban Rasha Vladimir Putin kan annobar Siberia.

WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu

Hukumar Lafiya ta Duniya ta buƙaci Rasha da ta samar da cikakken bayani bayan mutuwar wata ma'aikaciyar ɗakin gwaje-gwaje a wata cibiyar bincike kan annobar ciwon huhu a Siberia, yayin da Washington ke ƙara matsin lamba kan Moscow.

"Samar da bayanai a kan lokaci kuma cikin gaskiya a ƙarƙashin Dokokin Lafiya na Duniya yana da matuƙar muhimmanci don fayyace rahotanni masu karo da juna da kuma ba da damar yin duba sosai kan barazanar lafiyar jama'a," in ji Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Kazalika, kan batun, Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar a Fadar White House cewa zai yi magana kai-tsaye da Shugaban Rasha Vladimir Putin. 

"Ina da shirin kira, e," in ji Trump ga manema labarai, yana mai ƙarawa da cewa tattaunawar za ta kasance "nan ba da jimawa ba".

Rikicin diflomasiyya ya ta'azzara ne bayan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya buƙaci Moscow da ta fitar da bayanan da aka tabbatar da su a lokacin ziyarar da ya kai Iceland, yayin da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar da takardar diflomasiyya a hukumance wadda ke gargaɗin Rasha game da take dokokin lafiya na duniya.

Labarai masu cin karo da juna

Kamfanin dillancin labarai mai zaman kansa na Rasha ya ruwaito cewa wata ma'aikaciyar ɗakin gwaje-gwaje mai suna Darya Shipilova, mai shekaru 28, ta kamu da cutar Pneumonic Plague ta huhu bayan ta jefar da wani bututun gwaji mai ɗauke da ƙwayoyin cuta a Cibiyar Bincike da Yaƙi da Annoba ta Irkutsk da ke yankin Siberia da Gabas Mai Nisa, inda ya yi ikirarin cewa an killace mutane 200 da suka kamu da cutar.

Hukumomin Rasha sun yi watsi da rahoton da kakkausar murya, inda suka jaddada cewa binciken da aka gudanar bayan mutuwar da aka samu ya nuna babu wata ƙwayar cuta da ke da alaƙa da aikin Shipilova.

Cutar Pneumonic Plague, wata annobar huhu ce mai hatsarin gaske wadda ke yaɗuwa ta hanyar ƙwayoyin cutar, kazalika tana haifar da katsewar numfashi da mutuwa idan ba a yi maganinta da wuri ba.

A martanin da ta mayar wa saƙon Trump, Hukumar kare lafiyar jama'a da kare masu amfani da kayayyaki ta ƙasa ta Rasha, ta ce a shirye Moscow take ta taimaka wa Amurka da matsalolinta na kamuwa da cuta.

#