Sport
Dollar
43,4990
0.19 %Euro
51,6240
-0.9 %Gram Gold
6.788,9600
-9.85 %Quarter Gold
12.225,8700
-6.97 %Silver
116,5000
-28.39 %‘Wannan ɗanyen aiki wani ɓangare ne na ta'addanci da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi suka yi da gangan domin tayar da hankalin fararen-hula da lalata ababen more rayuwa,’ in ji shugaban hukumar Tarayyar Afirka.
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da harin da aka kai Filin Jirgin Saman Hamani Diori na birnin Yamai a Nijar, sannan ya jaddada goyon bayan hukumar ga gwamnatin Nijar.
Youssouf ya ce ya yi “matuƙar damuwa” bisa harin da ‘yanbindiga suka kai filin jirgin saman Yamai ranar Alhamis da daddare da kuma wanda suka kai ranar 18 ga watan Janairu a ƙauyen Bosiye da ke yammacin Nijar, inda suka kashe kimanin mutum 30.
“Wannan ɗanyen aiki wani ɓangare ne na ta'addanci da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi suka yi da gangan domin tayar da hankalin fararen-hula da lalata ababen more rayuwa,” in ji shugaban hukumar Tarayyar Afirka.
Ya jinjina wa jami’an tsaron Nijar bisa yadda suka “gaggauta mayar da martani” wanda ya taimaka wajen daƙile harin.
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka ya jaddada goyon bayan ƙungiyar ga al’ummar Nijar sannan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar.
Kazalika Youssouf ya yaba wa gwamnatin Nijar kan yaƙin da take yi da ta’addanci, inda ya bayar da misali game da yadda dakarun ƙasar suke fafutukar kawar da ‘yanta’adda.
Ya ce “an samu gagarumar nasara a samamen da dakarun ƙasar suka kai yankin Tillabéri,” wadda ya ƙara da cewa ta yi sanadin kashe ‘yanbindiga da dama tare da katse hanyoyin samun makamansu da kuma ƙwato kayan jama’a da suka sace.
Amurka ta kwashe ma’aikatan ofishin jakadancinta
Tuni dai Ma’aikatar Harkkin Wajen Amurka ta umarci kwashe ma’aikatan da aikinsu bai wajaba ba daga ofishin jakadancinta da ke Yamai da iyalansu saboda “hatsarin” da ka iya samunsu.
"Kada ku je Nijar domin yin kowace harka saboda rashin tsaro da ta’addanci da sace jama’a,” in ji wata sanarwar gargaɗi da Amurka ta tura wa ‘yan ƙasarta.
Comments
No comments Yet
Comment