Lamurra na baya bayan nan na zuwa ne yayin wata gagarumar ɓullar cutar Ebola a Jamhuriayr Dimokuraɗiyyar Kongo, wadda ta yaɗu zuwa wasu ƙasashen Afirka.

Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar

Uganda ta musanta samun cutar Ebola a ƙasarta bayan rahotanni sun ce wata ‘yar Nijeriya da ta bi ta ƙasar ta gabashin Afirka daga Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (DRC) ta kamu da Ebola.

A cikin watan sanarwar da ta fitar ranar Talata, ma’aikatar lafiya ta Uganda ta ce matar ta bi ta Uganda a farkon watan Oktoba ba tare da nuna alamu ba kuma alamun sun bayyana a jikinta ne bayan ta isa Nijeriya.

“Tafiya ta Uganda ba ya tabbatar da cewa an kamu da cuta a nan,” kamar yadda ma’aikatar ta faɗa, tana mai cewa har yanzu ana kan bincike game da inda ta kamu da cutar.

Uganda ta ce har yanzu Nijeriya ba ta ba da cikakken bayani ba game da jadawalin tafiyar matar da kuma tarihin lafiyarta domin taimakawa wajen ƙarin bincike da kuma duk wani ƙoƙari na nemo waɗanda suka haɗu da ita.

‘Babu mai cutar’

“Muna son mu bayyana cewa, a lokacin fitar da wannan sanarwar, Uganda ba ta da wanda aka tabbatar yana ɗauke da cutar Ebola,” in ji sanarwar.

Ma’aikatar ta ce za ta ƙarfafa tantancewa da kuma tsari na lafiyar jama’a a wuraren shiga, yayin da take kira ga jama’a su kwantar da hankulansu da kuma yawaita wanke hannayensu.

Ta ƙara da cewa an samar da taƙaitaccen matakai na tafiyar jinƙai da diflomasiyya.

Nijeriya ta tabbatar da wadda ta fara kamuwa da cutar Ebola a ɓullar cutar ta wannan lokacin ranar Talata, inda Ministan Lafiyar ƙasar Muhammad Ali Pate ya ce matar ta isa Abuja a wani jirgi na ƙetare daga Uganda.

An killace ‘yar Nijeriyar

An karɓi mara lafiyar ne a wani asibiti mai zaman kansa inda ta samu kulawa kafin a tabbatar da cewa ta kamu da cutar.

Daga baya aka killace ta, yayin da hukumomin lafiya suka fara neman mutum 44 da aka bayyana a matsayin waɗanda suka fi kusa da ita.

Abubuwan da suka faru a baya bayan nan na zuwa ne a cikin wata gagarumar ɓullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, wadda ta bazu zuwa wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Uganda.

Hukumomin Kongo sun ba da rahoton fiye da mutum 9,400 da suka kamu da cutar da kuma fiye da mutum 4,500 da suka mutu, lamarin da ya mayar da wanann ɓullar cutar Ebolar ɓullar cutar mafi muni a tarihin ƙasar.

Kenya ta kuma ba da rahoton waɗanda suka kamu da cutar a wani lamari da ke da alaƙa da ɓullar cutar, lamarin da ya sa hukumomin lafiya a faɗin yankin suka ƙarfafa sa iso da matakan mayar da martani.

#