Sport
Dollar
43,1952
0.04 %Euro
50,3297
0.05 %Gram Gold
6.405,7700
-0.39 %Quarter Gold
10.588,5400
-0.2 %Silver
125,5700
-3.05 %A lokacin zaɓen da ya gabata a 2021 Uganda ta katse intanet a faɗin ƙasar - zaɓen da aka yi zargin an tafka maguɗi sannan gwamnati ta musguna wa ‘yan adawa.
Uganda ta ba da umarnin katse intanet, kwana biyu kafin zaɓen da Shugaba Yoweri Museveni ke neman tsawaita mulkinsa na shekaru 40.
"Wannan matakin ya zama dole don rage yaɗuwar labaran ƙarya ta intanet cikin sauri, labaran ƙarya, zamba a lokcin zaɓe da kuma hatsarin da ke tattare da hakan, da kuma hana tayar da hankali da ka iya shafar amincewar jama'a da tsaron ƙasa a lokacin zaɓe," in ji Hukumar Sadarwa ta Uganda a cikin wata wasiƙa da ta aike wa masu samar da intanet a ranar Talata.
Dakatarwar za ta fara aiki da ƙarfe 6:00 na yamma agogon Uganda (15:00 GMT) kuma za ta ci gaba da aiki "har sai an bayar da sanarwar dawo da aiki," in ji UCC.
An kuma ƙara da cewa katse intanet ɗin ba zai shafi muhimman ayyukan gwamnati ba, in ji hukumar.
A lokacin zaben 2021 an katse intanet
Babu wata sanarwa daga gwamnati game da katse intanet ɗin. Jami'ai sun ce hukumomi ba sa son "yin tsokaci" kan wannan mataki da aka ɗauka.
Gwamnati ta yi alƙawarin cewa ba za a rufe intanet a lokacin zaɓen ba, tana mai bayyana wa a cikin wani rubutu da ta yi a ranar 5 ga Janairu cewa "da'awar da ke nuna akasin haka ƙarya ce, ɓatarwa ce, kuma an yi niyya ne don sanya tsoro da tashin hankali mara amfani a tsakanin jama'a."
A lokacin zaɓen da ya gabata a 2021 Uganda ta katse intanet a faɗin ƙasar - zaɓen da aka yi zargin an tafka maguɗi sannan gwamnati ta musguna wa ‘yan adawa, ƙarƙashin jagorancin mawaƙi Bobi Wine, wanda ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Comments
No comments Yet
Comment