Sport
Dollar
42,8044
0.17 %Euro
50,1756
-0.07 %Gram Gold
5.973,2500
0.3 %Quarter Gold
9.852,9100
0.24 %Silver
92,4600
2.85 %Jirgin kayan ya isa Port of Sudan inda aka tarbe shi ta hannun Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Bala'o'i da Ayyukan Gaggawa ta Turkiyya (AFAD), Hamza Taşdelen, da jakadan Turkiyya a Sudan, Fatih Yıldız.
Turkiyya ta isar da tantuna 10,000 cikin 30,000 da za ta kai Sudan a matsayin agaji domin taimakawa don magance matsalar da ake fama da ita ta ƙarancin matsugunai a ƙasar.
Jirgin kayan ya isa Port of Sudan inda aka tarbe shi ta hannun Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Bala'o'i da Ayyukan Gaggawa ta Turkiyya (AFAD), Hamza Taşdelen, da jakadan Turkiyya a Sudan, Fatih Yıldız.
Wasu da suka halarci taron sun hada da Kwamishinan Hukumar Agajin Jinƙai ta Sudan Selva Adem, Shugaban Ofishin IOM a Sudan Mohamed Refaat, da sauran jami'an Sudan.
Sojojin Sudan na yaƙi da dakarun RSF tun Afrilun 2023, bayan rushewar gwamnatin haɗaka ta riƙon ƙwarya a ƙasar.
Tun daga lokacin, rikicin ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin babbar annobar jinƙai a duniya a yau.
An ɗauko tantunan tun daga tashar Mersin ta Turkiyya a ranar 6 ga Disamba. Taşdelen ya ce za a yi jigilar kusan tantuna 30,000 inda za a raba jigilar zuwa rukuni uku, kuma Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta MDD ta kuduri aniyar isar da tantunan zuwa ga waɗanda suka fi mutukar buƙata.

'Ba ma kallon su kawai a matsayin kayan agaji. Waɗannan suna ɗauke da saƙonni masu dumi cewa mutanen Turkiyya suna cewa "Muna tare da Sudan da 'yan Sudan' a lokutan wahala. Haka kuma alama ce ta tsohuwar abota mai ƙarfi tsakanin Turkiyya da Sudan,' in ji jakadan Turkiyya Yıldız.
Ya ƙara da cewa: 'Sudan da Turkiyya za su ci gaba da buƙatar juna a matsayin abokai da 'yan'uwa. Turkiyya na tare da 'yan Sudan ba tare da neman komai a madadin haka ba.'
Kwamishinan Hukumar Agajin Jinƙai ta Sudan, Adem, ya nuna godiya ga Turkiyya kan babban tallafi da taimakon da aka bayar ga 'yan Sudan.
Kwamishinan Agajin Jinƙai na Sudan Selva Adem ya ce gwamnatin Sudan za ta yi aiki domin sauƙaƙe isar da dukkan agajin jinƙai.
'Muna tabbatar da cewa za a kai tallafin zuwa ƙauyuka, sansanoni da kowane yanki da ake bukata. An riga an kai taimako a baya ga masu bukata, kuma tsarin yana da cikakken gaskiya,' in ji Adem.
Shugaban ofishin IOM a Sudan, Refaat, ya jaddada cewa an shirya shirin raba kayan cikin hadin gwiwa da gwamnatin Sudan da AFAD, ya kuma ce za a samar da hadin kai da ake bukata domin isar da mafi yawan tantunan ga masu bukata a yankunan Darfur ta Arewa da Kordofan.
Refaat ya kara da cewa Turkiyya ce ƙasa ta farko kuma ita kadai ce da ta bai wa yankin Tawila tantuna, inda mutanen da aka tilasta barin Al Fasher suka nema mafaka.
Comments
No comments Yet
Comment