Sport
Dollar
40,7086
0.17 %Euro
47,4348
-0.19 %Gram Gold
4.444,4400
0.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ƙasashen biyu sun sha alwashin haɗa gwiwa a yunƙurin shawo kan ƙalubalen da yankin Gabas ta Tsakiya yake fama da shi, a cewar Ministan Harkokin Wajen Masar.
Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya sanar ranar Asabar cewa suna haɗa gwiwa da Tukiyya a hanyoyin warware rikice-rikicen da ke addabar yankin, bayan ganawar da ya yi da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a El Alamein, Masar.
A wani taron manema labarai na haɗin gwiwa, Abdelatty ya bayyana halin da ake ciki a dangantakar Masar da Turkiyya a matsayin “muhimmin mataki na alaƙa mai ƙarfi.”
Ministocin biyu sun tabbatar da “amincewa da yunƙurin haɗa kai tare da yin amfani da dukkan dama wajen tunkarar shirin Isra’ila na mamaya da kuma tasirinsa,” in ji shi.
Taron gaggawa na OIC
Fidan ya ce Turkiyya za ta kira taron gaggawa na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai wato Organization of Islamic Cooperation (OIC) domin tattauna shirin Isra’ila na cikakkiyar mamaya a Gaza.
Comments
No comments Yet
Comment