Yayin da yake bayyana fatan nasarar haɗin kan Pakistan da Turkiyya, ministan man fetur na Pakistan ya ce mahukuntan Islamabad sun jajirce wajen ba da “cikakkken goyon baya” da “ba da ƙarin gwiwa” ga irin wannan aiki na nemo mai a tekun ƙasarsu.

Turkiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar neman iskar gas a teku

Turkiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar neman mai da iskar gas a wuraren haƙar mai 40 a ƙasar da ke kudancin nahiyar Asiya.

An rattaba wa yarjejeniyar hannu ne ranar Talata a lokacin da ake taron shekarar 2025 na zuba jari a fannin ma’adinan Pakistan a babban birnin ƙasar Islamabad, in ji wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen Pakistan.

A watan Fabrairu, gwamnatin ƙasar Pakistan ta yi shelar ba da damar neman lasisin haƙar mai a wurare 40 a filayen da ke gefen kogunan Makaran da Indus, in ji sanarwar.

“Wannan aniya ta neman lasisin dama ce mai muhimmanci wajen jan hankalin masu zuba jari a fannin makamashin ƙasar,” in ji sanarwar.

Kamfanin mai na Mari Energies Limited da kuma kamfanin mai na ƙasar Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejejniyar da kamfanonin ƙasar Turkiyya, Türkiye Petrolleri  da Anonim Ortaklığı (TPAO), domin su nemi lasisin haƙar man tare.

“Mun yi imanin cewa wannan haɗin gwiwar zai janyo zuba jarin da Pakistan ke ɓukata kuma zai ba da damar ƙara wa juna sani kan fasaha da ƙwarewa domin kai Pakistan ga matakin da ya kamata ta cim ma wajen haƙa da kuma amfani da ma’adinanta na ɓangaren cikin ruwa,” in ji sanarwar.

Minsitan makamashi da ma’adinai na Turkiyya Alparslan Bayraktar tare da ministan man fetur na Pakistan Ali Pervaiz Malik sun halarci bikin rattaba hannun.

Yayin da yake fatan nasarar haɗin kan Pakistan da Turkiyya, Malik ya ce Islamabad ta tsaya tsayin daka domin ba da “cikakken goyon baya” tare da “ba da ƙwarin gwiwa ” ga irin wannan ƙoƙari na haɗin gwiwa domin nemo mai a tekunta.

Bayraktar ya yaba wa shirya taron zuba jari a fannin ma’aidinai da mahukuntan Islamabad suka yi.

 

#