Idan ruwa ya yi kasa a jikin ɗan'adam zai ji bakinsa yana yawan bushewa sannan yawan fitsarinsa zai ragu ya kuma yi duhu, hakan na iya haifar da rashin ƙarfin jiki da ciwon kai da tashin zuciya da amai da dai sauransu, in ji wani likita a Nijeriya.

Tsananin zafi: Mai azumi na buƙatar ruwa sosai a jikinsa — Masana a Nijeriya

Masana a Nijeriya sun gargadi masu azumtar watan Ramadan a wannan shekarar kan su yawaita shan ruwa, sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi da ka iya haifar da cututtuka sakamakon rashin wadataccen ruwa a jiki, musamman ga masu aikin ƙarfi ko wahala a wuraren da zafin rana ya yi yawa.

A wata sanarwa da Hukumar kula da bayar da rahotannin yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta fitar a shafinta na X a watan Fabrairu, ta yi hasashen cewa yankin arewa zai fuskanci tsananin zafin da ya kai maki sama 41 a ma'aunin salshiyas, sannan sama da maki 39 a yankin kudancin kasar.

Azumin bana ya riski al'ummar Musulmai a jihohin Nijeriya a irinsu Kano da Sokoto da Zamfara da babban birnin tarayya cikin tsananin zafi, kuma tuni likitoci irin su Dakta Muhammad Dauda Haroon na asibitin koyarwa na ATBU da ke jihar Bauchi, ya ce an fara kai musu marasa lafiya da tsananin zafin ya yi wa illa, waɗanda kuma sun ɗauki azumi a bakinsu.

''Irin wannan yanayin ya fi ƙamari kan masu aikin ƙarfi, ko waɗanda suke gudanar da sana'o'insu cikin yanayin tsananin rana,'' in ji Dakta Muhammad Dauda Haroon.

Likitan ya ƙara da cewa ''Idan ruwa ya yi ƙasa a jikin ɗan'adam zai dinga jin bakinsa yana yawan bushewa, sannan yawan fitsarinsa zai ragu ya kuma yi duhu, hakan na iya haifar da matsalolin rashin ƙarfin jiki da ciwon kai da tashin zuciya da amai da dai sauransu'', kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka Hausa.

Da yake magana da TRT Afrika, Sheik Muhammad Bin Uthman, wani malamin addinin Musulunci da ke birnin Kano na arewacin Nijeriya, ya shawarci Musulmai su sha ruwa sosai a lokacin yin sahur da buda-baki.

Ya ce "Wannan zai rage musu tsananin ƙishi ruwan da ka iya shafar walwalarsu a yayin da suke azumi a tsananin zafi”.

Ya ƙara da cewa, “A yanayi na matukar takura, ya halatta Musulmi ya karya azuminsa idan azumin zai iya zamowa hadari ga lafiya ko rayuka, musamman idan karya azumin shi ne kadai mafita a gare shi”.

Dakta Muhammad ya bayyana cewa akwai yiwuwar ɓarkewar cututtuka masu alaƙa da zafi da kuma ƙarancin ruwa a jikin ɗan'adam wadanda suka hada da cutar sanƙarau da ƙyanda har da suma a wasu lokutan.

#