Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

Shugaban Kasar Amurka ya yi alkawarin kawo karshen takardun ‘dukkan ‘yan gudun hijira ba bis aka’ida ba da Biden ya karba zuwa kasar’.

Trump ya ce Amurka za ta dakatar da hijirar 'yan cirani daga kasashe marasa arziki har abada

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Alhamis ya gabatar da wani sabon shiri game da shige da fice, inda ya ayyana dakatar da hijira har abada daga abin da ya bayyana a matsayin "Ƙasashe na Duniya na Uku" wato kasashe matalauta.

Trump bai ambaci sunan wata ƙasa ba ko kuma ya bayyana abin da yake nufi da ƙasashen duniya na uku ko kuma "dakatar da shirin har abada"

Ko da yake mun ci gaba a fannin fasaha, manufofin shige da fice sun lalata waɗannan fa'idodi da yanayin rayuwa ga mutane da yawa, in ji Trump.

"Zan dakatar da gudun hijira zuwa Amurka har abada daga dukkan ƙasashen duniya matalauta don ba da damar tsarin Amurka ya murmure gaba ɗaya," in ji Trump a shafinsa na sada zumunta na Truth Social.

Trump ya kuma yi alƙawarin sauya yawancin manufofin da suka shafi shige da fice da aka aiwatar a ƙarƙashin gwamnatin Biden da ta gabata.

Shugaban ya ce zai "dakatar da duk miliyoyin shiga Biden ba bisa ƙa'ida ba, gami da waɗanda alkalamin Joe Biden ya sanya wa hannu, kuma ya kori duk wanda ba kadara ta gaske ba ne ga Amurka, ko kuma ba zai iya ƙaunar ƙasarmu ba."

Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da aka gano wani ɗan ƙasar Afghanistan, Rahmanullah Lakanwal, a matsayin wanda ake zargi da harbin bindiga a wani hari da ya kashe wani sojan Tsaron Kasar da kuma raunata wani a kusa da Fadar White House ranar Laraba.

Bayan lamarin, Amurka ta sanar da cewa ta dakatar da duk wani aikin shige da fice ga 'yan ƙasar Afghanistan.

Trump ya ce zai kawo ƙarshen duk wani tallafi na tarayya da tallafin da zai bai wa waɗanda ba 'yan ƙasar Amurka ba, sannan zai "hana 'yan ci-rani da ke kawo cikas ga zaman lafiyar cikin gida, sannan zai kori duk wani ɗan ƙasar waje da ke fuskantar tuhuma daga gwamnati, mai hatsarin tsaro, ko kuma wanda bai dace da wayewar Yammacin duniya ba."

Ya tsara shirin nasa a matsayin wani ɓangare na wani babban ƙoƙari da ya kira "juyar da hijira," wanda ya bayyana a matsayin tilas don dawo da zaman lafiyar ƙasa.

"Za a ci gaba da dabbaka waɗannan manufofi da nufin cim ma babbar raguwar yawan jama'a ba bisa ƙa'ida ba da kuma masu tayar da hankali, gami da waɗanda aka karbe su ta hanyar da ba ta bisa ƙa'ida ba. Kawar da gudun hijira ce kawai za ta iya magance wannan yanayi gaba ɗaya," in ji shi.

Shugaban ya haɗa sanarwar manufofin da saƙon ranar hutu, yana taya murna da fatan alheri yayin da yake ba da gargaɗi ga waɗanda ya zarga da lalata ƙa'idodin Amurka.

"Bayan haka, ina taya murnar wannan rana amma banda ga waɗanda suka tsani Amurka, suke yin sata, kisan kai da lalata duk wani abu da Amurka ke kare wa, in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#