Ƙungiyar ta ce adadin waɗanda aka kwantar domin jinyar tamowa ya tashi daga kusan 17,000 a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 zuwa kusan 20,000 a makamancin lokacin shekarar 2026.

Tamowa ta ƙaru a arewa maso gabashin Nijeriya da kaso 18 cikin 100, in ji Red Cross

Ƙungiyar Bayar da Agajin Lafiya ta Red Cross (ICRC) ta ce yawan mutanen da aka samu suna fama da tamowa a cibiyoyin lafiya shida da asibitoci huɗu da take tallafawa a arewa maso gabashin Nijeriya ya ƙaru da kashi 18 cikin ɗari tsakanin watan Janairu da Satumba na shekarar 2026, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2025.

Ƙungiyar ta ce adadin waɗanda aka kwantar domin jinyar tamowa ya tashi daga kusan 17,000 a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 zuwa kusan 20,000 a makamancin lokacin shekarar 2026. Ƙananan yara, mata masu juna biyu da mata masu shayarwa ne suka fi fuskantar matsalar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin saƙon da jami’in hulɗa da jama’a na ICRC a Abuja, Aliyu Dawobe, ya fitar domin bikin Ranar Abinci ta Duniya.

A cewar sanarwar, Mubi da ke jihar Adamawa ce ta fi samun ƙaruwa mafi yawa, inda adadin waɗanda aka kwantar saboda tamowa ya ƙaru da kusan kashi 24 cikin ɗari, daga kusan mutane 4,600 tsakanin Janairu da Satumba na shekarar 2025 zuwa kusan 5,700 a makamancin lokacin shekarar 2026.

Ƙungiyar ta danganta ƙarin masu fama da tamowa da illolin rikice-rikicen makamai, sauye-sauyen yanayi da matsin tattalin arziki, waɗanda suka kawo cikas ga hanyoyin samun abin rayuwa tare da rage damar iyalai ta samun isasshen abinci.

Sanarwar ta ambato wani manomi, Saminu Samiyu Ijaduwa, yana cewa ababen fashewa da rashin tsaro sun hana shi samun damar zuwa gonarsa cikin sauƙi, lamarin da ya tilasta masa yin noma a wani ƙaramin fili kusa da gidansa.

“Saboda rikicin, fita kilomita ɗaya daga gari domin yin noma na iya zama haɗari sosai. Wataƙila ba za ka dawo ba!” in ji shi.

ICRC ta ce tana aiki tare da Red Cross ta Nijeriya wajen tallafawa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 15 da asibitoci huɗu, tare da taimaka wa al’ummomi fiye da 200 wajen magance tamowa da ƙarfafa samar da isasshen abinci.

 

 

#