Dollar

41,9666

0.05 %

Euro

48,8764

0.14 %

Gram Gold

5.454,0200

-1.65 %

Quarter Gold

9.656,3500

0 %

Silver

64,5300

-1.65 %

Rikici tsakanin Sojojin Sudan da dakarun RSF ya ƙara ƙazancewa a yankunan Kordofan da Darfur a ‘yan makonnin nan.

Sudan ta nemi al'ummar duniya su yi Allah wadai da 'laifukan' da RSF ke aikatawa kan fararen-hula

Sudan ta yi kira ga al'ummar duniya da kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama su yi Allah wadai da “laifuka” da dakarun Rapid Support Forces (RSF) ke aikatawa kan fararen-hula, tare da ɗaukar matakin gaggawa don dakatar da su.

“Gwamnatin Sudan tana Allah wadai da laifuka da kuma take hakkin bil’adama da dakarun ‘yan tawaye na Rapid Support Forces ke ci gaba da aikatawa kan fararen-hula marasa makami, da kuma lalata cibiyoyin gwamnati da gangan, wanda ya saɓa wa dukkan ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da daɓi’un bil’adama,” in ji sanarwar majalisar gwamnatin ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnati tana kira ga al’ummar duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama su yi Allah wadai da waɗannan munanan ayyuka, su ɗauki matakin gaggawa don dakatar da laifukan wannan ƙungiya, tare da gurfanar da masu aikata laifukan a gaban shari’a, domin kare fararen-hula da tabbatar da haƙƙin ɗan’adam.”

“Kai hari kan fararen-hula da muhimman wurare na wakiltar wata babbar barazana da kuma wani hari kai tsaye wanda ke barazana ga tsaron jama’a, yana zama laifin yaki, kuma ya saɓa wa dukkan dokokin ƙasa da ƙasa da na jin ƙai,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Har zuwa karfe 2000 GMT, dakarun Rapid Support Forces ba su fitar da wata sanarwa kan wannan batu ba.

Tun da farko a ranar Asabar, sojojin Sudan sun sanar da cewa sun daƙile wani babban hari da RSF ta kai a Al Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, daga ɓangarori biyar, a ɗaya daga cikin mafi zafafan arangama da birnin ya gani cikin watanni.

A makonnin baya-bayan nan, faɗa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya ƙara tsananta a yankunan Kordofan da Darfur.

Sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun fara faɗa tun watan Afrilun 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20,000 tare da raba mutane miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin cikin gida.

Duk da haka, bincike daga jami’o’in Amurka ya ƙiyasta adadin waɗanda suka mutu ya kai kimanin 130,000.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#