Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaryata wani rahoto na bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya yi zargin cewa an sace wani Birgediya Janar a Borno.

Sojojin Nijeriya sun daƙile kwanton-ɓauna, sun yi watsi da jita-jitar sace wani janar na soja

Sojojin haɗaka na Brigade ta 25 da ke sintiri domin kare al’ummomi a yankin Wajiroko da ke Azir–Multe, cikin Karamar Hukumar Damboa a Borno, sun fuskanci kwanton-ɓauna mai tsanani daga ‘yan ta’adda a ranar Juma’a yayin da suke komawa bayan nasarar da suka samu a kusa da dajin Sambisa.

Rundunar, wadda Brigediya Janar M. Uba, Kwamandan Brigade ta 25, ya jagoranta, ta haɗa da sojoji da kuma jami’an kare farar-hula na Civilian Joint Task Force (CJTF), kamar yadda rundunar sojin Nijeriya ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Duk da irin ƙarfi da ƙwaƙƙwaran harbin da suka sha, sojojin sun mayar da martani da iya ƙarfinsu, suka daƙile kwanton-ɓaunar, sannan suka tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa cikin ruɗani tare da barin shirin da suka zo da shi.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyu da kuma mambobin CJTF biyu sun rasa rayukansu a yayin arangamar. Rundunar Sojan ta bayyana su a matsayin “jarumai masu kishin ƙasa,” tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai da abokan aikinsu kan wannan sadaukarwa ta ƙarshe da suka yi wa Nijeriya.

Haka kuma rundunar sojin ƙasar ta kuma ƙaryata wani rahoto na bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta da ya yi zargin cewa an sace Birgediya Janar ɗin da ke jagorantar rundunar.

Rundunar sojin ta buƙaci jama’a da su yi watsi da wannan labari na ƙarya, tare da tabbatar da cewa kwamandan yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana kan aikinsa yadda ya kamata.

Haka kuma Shugaban Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya yaba da jaruntaka, juriya, da sadaukarwar sojojin.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#