Sport
Dollar
42,3350
0.2 %Euro
49,1712
0.05 %Gram Gold
5.547,4900
-0.07 %Quarter Gold
9.430,0100
0 %Silver
69,2000
0.51 %Wannan ne karon farko da gwamnatin Kano za ta gabatar da kasafin kuɗi da ya haura naira tiriliyan ɗaya, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan na Kano Sanusi Bature ya fitar ranar Juma’a.
Gwaman Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce zai gabatar da kasafin kuɗin shekara mai zuwa ta 2026 da ya haura naira tirilyan daya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Juma’a ta ce wannan ne karon farko da gwamnatin Kano za ta gabatar da kasafin kuɗi da ya haura naira tiriliyan daya.
Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke buɗe Taron Majalisar Zartarwa na Musamman don tattaunawa kan ƙudirin kasafin kuɗin na badi, wanda za a mika shi ga majalisar dokokin jihar a makon gobe.
Gwamna Abba ya ce kasafin kuɗin zai mayar da hankali kan ci gaba da ayyukan da ake yi yanzu, da sabunta birane da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.
Sauran ɓangarorin da za a bai wa muhimmanci a cewar sanarwar sun haɗa da bunƙasa gidaje da aikin gona da ilimi da tallafa wa matsakaita da kananan masana’antu, da nufin haaɓka tattalin arzikin jihar.
Ya ƙara da cewa girman kasafin kuɗin yana da dangantaka da bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, da kuma toshe hanyoyin da kueɗaɗn gwamnati ke zurarewa.
Comments
No comments Yet
Comment