Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kalaman da Aliko Dangote ya yi na zargin kashe miliyoyin daloli wajen biyan kudin makarantar sakandare ga 'ya'yan Farouk Ahmed a ƙasashen waje.
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur a Nijeriya, NMDPRA, Farouk Ahmed ya yi murabus a cewar fadar shugaban Nijeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar da maraicen Larabar nan.
Sanarwar, wacce Mai Bai wa Shugaba Tinubu Shawara na Musamman kan Watsa Labarai Bayo Onangu ya fitar ta ce tuni shugaban ya miƙa sunan Injiniya Saidu Aliyu Muhammed ga Majalisar Dattijai don tantance shi a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban, Farouk.
Haka kuma sanarwar ta ce shi ma shugaban Hukumar NUPRC wacce takwara ce ga NMDPRA Gbenga Komolafe ya yi murabus, kuma shi ma tuni aka miƙa sunan Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan domin maye gurbinsa.
“Domin cike gurbin da suka bari, Shugaba Tinubu ya rubutawa Majalisar Dattijai wasiƙa yana neman ta gaggauta ɗaukan matakin tabbatar da Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin shugabar NUPRC da Injiniya Saidu Aliyu Muhammed a matsayin shugaban NMDPRA,” a cewar sanarwar.
Duka mutanen biyu da suka ajiye aiki Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ne ya naɗa su muƙaman a 2021.
Gagarumin zargi daga Dangote
Sai dai sanarwar ta Bayo ba ta ambaci dalilin saukar ta su ba, sannan babu wani karin bayani.
Amma matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kalaman da Aliko Dangote ya yi na zargin kashe miliyoyin daloli wajen biyan kudin makarantar sakandare ga 'ya'yan Farouk Ahmed.
Tuni dai Dangote ya miƙa wa hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya, ICP ƙorafi kan shugaban Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, Ahmed Farouk, kan zarginsa da cin hanci da kuma almubazzaranci da dukiya.
A cikin takardar ƙorafin da aka gabatar a ranar 16 ga Disamba, Dangote ya nemi a kama Ahmed, a gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya bisa zarginsa da yin rayuwar ƙarya fiye da ƙarfinsa a matsayin ma'aikacin gwamnati.
A cikin takardar ƙorafin, wadda ofishin Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN) ya samu, Dangote ya zargi shugaban NMDPRA da kashe fiye da dala miliyan bakwai ba tare da wata shaida ta halastacciyar hanyar samun kuɗaɗen shiga ba, har na tsawon shekaru shida kafin a biya kudin makarantar 'ya'yansa hudu a makarantu daban-daban a Switzerland.
Har kawo yanzu dai Farouk bai mayar da martani kan zargin na Dangote ba, amma dai ya fitar sanarwa yana musa cewa shi ne ya fitar da wani martani da aka ringa yaɗawa a shafukan sada zumunta da sunan Farouk ɗin ne ya fitar.
Amma dai a sanarwar ta Laraba wacce aka wallafa a shafukan sada zumunta na NMDPRA, Farouk ya ce ba zai mayar da martani ba a bainar jama’a, amma ya ji daɗi da yake “wanda ya yi zargin ya nemi hukuma ta gudanar da bincike. Na yi imani cewa hakan zai bayar da dama a fayyace batun a kuma wanke ni,” in ji Farouk Ahmed.
Comments
No comments Yet
Comment