Dollar

42,2643

0.04 %

Euro

49,0932

0.18 %

Gram Gold

5.716,6300

0.33 %

Quarter Gold

9.512,1700

0 %

Silver

73,1500

1.08 %

Bayan ziyarar ba-zata da Lionel Messi ya kai filin wasan Barcelona, shugaban ƙungiyar, Joan Laporta ya amsa tambaya kan yiwuwar dawowar Messi a Janairu.

Shugaban Barcelona ya gwale Messi kan yiwuwar komawarsa Barca

Ana ci gaba da yaɗa jita-jitar cewa tsohon ɗanwasan Barcelona, Lionel Messi ya kama hanyar komawa ƙungiyar a matsayin aro a Janairu mai zuwa.

Batun na zuwa ne bayan da aka ga Messi ya kai wata ziyarar ba-zata zuwa filin wasan Barca na Camp Nou da aka kammala gyarawa, inda yake jaddada soyayyarsa ga kulob ɗin.

Messi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa, "Ina fatan wata rana na dawo [filin] nan, ba wai don yin bankwana ba, saboda ban yi hakan a baya ba…".

Wannan ne ya sa aka tambayi shugaban Barcelona, Joan Laporta kan hakan, amma kai-tsaye sai bai nuna amincewa da burin Messi ba.

Laporta ya ce, "Saboda girmamawa ga Messi, da kuma ‘yan wasanmu, da mambobinmu, wannan ba lokacin yin hasashe kan abin da ba zai yiwu ba ne."

Taron karramawa

Sai dai shugaban ya ce Barcelona na nan tana shirin yin taron karramawa ga Lionel Messi, da zarar an kammala sake buɗe filin wasansu.

A 2021, Messi ya yi ƙaura daga Barca zuwa Paris Saint-Germain babu shiri, sakamakon cewa ƙungiyar ba ta da kuɗin ba shi sabuwar kwantiragi.

A cewar Laporta, taron karrama Messi zai zama abin da ya fi dacewa don ƙaddamar da filin wasan na Camp Nou da aka sabunta.

A ɓangarensa, Messi ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da ƙungiyar da yake wa wasa a yanzu, Inter Miami ta Amurka, wadda za ta kai 2028.

A halin yanzu dai Messi na tare da tawagar ƙasarsa Argentina, wadda ke shirin buga wasan sada zumunta da Angola ranar Jumma’a, 14 ga Nuwamban 2025.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#