Tan miliyan ɗaya na waken soya da tan 200,000 na jan nama Saudiyyar ke so a duk shekara daga Nijeriya. Ministan Ayyukan Gona na Nijeriyar ya tabbatar da cewa hakan ba zai shafi nama da waken soyar da ake samarwa a ƙasar ba.
Ministan Ayyukan Gona na Nijeriya Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa ƙasar Saudiyya ta nuna sha’awarta wajen sayen waken soya da jan nama daga Nijeriya.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Asabar inda ya ce takwaransa ministan aikin gona na Saudiyya ne ya bijiro masa da wannan buƙata a wata ziyara ta kwana biyu da ya kai Nijeriya.
Kyari ya ce Saudiyyar na son sayen aƙalla tan 200,000 na jan nama a duk shekara daga Nijeriya sai kuma tan miliyan ɗaya na waken soya.
Ya kuma bayyana cewa a shirye Saudiyyar take ta taimaka wa Nijeriya wurin kafa kamfanonin da za su rinƙa ƙera kayayyakin aikin gona a ƙasar.
Ministan ya bayyana cewa a Nuwambar 2023 ne ya kai ziyara ƙasar Saudiyya inda har ya tattauna da ministan aikin gona na ƙasar a yayin taron da Saudiyya ta shirya na na ƙasashen Afirka.
Ya bayyana cewa a gefen taron ne ya samu ya tattauna da ministan kan yadda za a kawo ci gaba a ɓangaren aikin gona.
“Bayan tattaunawar da muka yi mai armashi, Ministan Aikin Gona na Saudiyya ya kawo ziyara Najeriya. A lokacin ziyarar tasa ta kwana biyu, mun shirya tattaunawa da ‘yan kasuwarmu da ke harkar gona. Wannan tattaunawar ta yi armashi sosai wadda ta haifar da fahimtar juna a tsakani,” in ji Kyari.
“Ba da jimawa ba bayan zuwansa, mun samu buƙatar Saudiyya inda suka nuna suna son tan 200,000 na jan nama a duk shekara, da kuma tan miliyan ɗaya na waken soya. Ina son na tabbatar da cewa samar da waɗannan kayayyaki masu kyau ba za su shafi waɗanda ake amfani da su a Nijeriya ba,” in ji shi.