Sport
Dollar
41,9632
0.12 %Euro
48,9529
0.09 %Gram Gold
5.861,8500
2.35 %Quarter Gold
10.085,5000
0.77 %Silver
70,7200
1.18 %A farkon wannan watan, rundunar sojojin ta bayyana cewa "wani atisaye na yau da kullum ya haifar da kama jami'ai goma sha shida kan batutuwan rashin ɗa'a da kuma karya dokokin aiki."
Rundunar Tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kama jami’ai 16 kan zargin yunƙurin juyin mulki, inda suka ƙalubalanci rahotannin kafofin watsa labarai na cikin gida.
Ƙasashen yammacin Afirka, ciki har da Nijeriya, sun sha fama da juyin mulki a tarihi, inda ƙasar ta shafe mafi yawan shekarunta bayan samun ‘yancin kai a ƙarƙashin mulkin soja tun bayan samun 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1960.
Sabon juyin mulki zai mayar da hannun agogo baya a Nijeriya, bayan fiye da shekaru ashirin da biyar na dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.
"Rundunar Sojojin Nijeriya tana so ta bayyana ƙarara cewa iƙirarin da aka yi a labarin da aka wallafa ba gaskiya ba ne gaba ɗaya," in ji wata sanarwa daga Tukur Gusau, daraktan watsa labarai na Rundunar Tsaron Nijeriya, ba tare da bayyana wace kafar watsa labarai yake nufi ba.
Amma Sahara Reporters, wata kafar yada labarai ta yanar gizo, da kuma Premium Times, wadda ke da hedikwata a Abuja, sun ce aƙalla jami'ai 16 suna yi niyyar kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda ya hau mulki a shekarar 2023 bayan lashe zabe.
‘Bincike na cikin gida’
Tun da farko rundunar sojin ta sanar da cewa an kama jami'ai 16 kan "batutuwan rashin ɗa'a".
Kafofin watsa labarai biyu, suna ambaton majiyoyin tsaro, sun ruwaito cewa kamun yana da alaƙa da zargin yunƙurin juyin mulki.
A farkon wannan watan, rundunar sojojin ta bayyana cewa "wani atisaye na yau da kullum ya haifar da kama jami'ai goma sha shida kan batutuwan rashin ɗa'a da kuma karya dokokin aiki."
Sanarwar sojojin ta kara da cewa: "Bincike ya nuna cewa korafinsu ya fi yawa ne kan rashin samun ƙarin girma saboda gazawa a jarrabawar ƙarin girma, tare da wasu matsaloli."
A cikin sanarwar ranar Asabar, Gusau ya ce binciken "wani tsarin cikin gida ne na yau da kullum wanda aka yi domin tabbatar da cewa an kiyaye ɗa'a da ƙwarewa a cikin rundunar."
Comments
No comments Yet
Comment