Sport
Dollar
41,9660
0.13 %Euro
48,9288
0.04 %Gram Gold
5.826,3400
1.73 %Quarter Gold
10.120,0200
1.12 %Silver
71,1000
1.73 %Bayanai sun nuna cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe kwamandan soji na runduna ta 202 da ƙananan sojoji biyar da ‘yan Civilian Joint Task Force (JTF) guda uku a ƙauyen Kashimiri na ƙaramar hukumar Bama a wani harin kwanton-ɓauna da suka kai musu.
Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojojin Nijeriya aƙalla bakwai a wani hari da suka kai a arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar a ƙarshen mako.
’Yan ta’addan sun kai harin ne kan dakarun tsaron a yankin Bama na Jihar Borno, lamarin da ya janyo mutuwar sojoji aƙalla bakwai, yayin da wasu daga cikinsu suka ji raunuka kuma aka kai su asibiti.
Jaridun ƙasar irin su Daily Trust sun rawaito cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe kwamandan soji na runduna ta 202 da ƙananan sojoji biyar da ‘yan Civilian Joint Task Force (JTF) guda uku a ƙauyen Kashimiri na ƙaramar hukumar Bama a wani harin kwanton-ɓauna da suka kai musu.
Bayanai sun nuna cewa an yi wa sojojin kwanton-ɓauna ne a yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Bama bayan sun gudanar da wani gagarumin aikin kawar da gyauron ‘yan ta’adda ranar Jumma’a.
Ƙungiyar Boko Haram, wadda aka kafa a Nijeriya tun farkon shekarun 2000, ta ƙaddamar da hare-hare masu muni tun shekarar 2009, lamarin da ya kashe dubban mutane.
Ƙungiyar ta kuma faɗaɗa hare-harenta zuwa ƙasashen Kamaru da Chadi da Nijar masu maƙwabtaka tun shekarar 2015, inda ta kashe aƙalla mutum 2,000 a yankin tafkin Chadi.
Tashin hankali da arangama ta sa ɗaruruwan dubban mutane sun ƙurace daga gidajensu a faɗin Nijeriya.
Comments
No comments Yet
Comment