Dollar

42,2340

0.05 %

Euro

48,8169

-0.13 %

Gram Gold

5.534,9300

1.86 %

Quarter Gold

9.222,3300

0 %

Silver

67,3400

2.46 %

Ƙungiyar Likitocin Sudan ta ce: "RSF ta tattara ɗaruruwan gawawwaki daga tituna da unguwannin birnin, suka binne wasu cikin kabarun bai-ɗaya sannan kuma suka ƙone wasu a wani yunƙurin ɓoye shaidar laifukan da suka aikata wa fararen-hula."

RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan

Ɗaruruwan fararen-hula ne dakarun RSF suka binne cikin kabarin bai-ɗaya yayin da ƙone wasu a birnin Al-Fasher da ke yammacin Sudan, a ranar Lahadi.

Ƙungiyar Likitocin Sudan ta ce: "RSF ta tattara ɗaruruwan gawawwaki daga tituna da unguwannin birnin, suka binne wasu cikin kabarun bai-ɗaya sannan kuma suka ƙone wasu a wani yunƙurin ɓoye shaidar laifukan da suka aikata wa fararen-hula."

Ta kwatanta binne fararen-hula a matsayin "cikakken kisan kiyashi" kuma ta ce wannan yana "keta dukkan ƙa'idodin duniya da na addini da ke haramta lalata gawawwaki da kuma bayar da dama a binne gawa a cikin mutunci.”

"Halin da ake ciki a Al-Fasher ya wuce matsananciyar masifa ta jin kai; ya zama kisan kiyashi kai tsaye ga rayuwa da mutuncin ɗan adam a cikin wani yanayi na shiri da duniya ta yi wanda kusan ya zama nau'i na haɗin baki," in ji bayanin.

'Ba za a iya goge laifuka ba'

"Ba za a iya goge laifukan RSF ta hanyar binne ko ƙone gawawwaki ba," in ji ƙungiyar likitocin, tana kiran al'ummar duniya da su ɗauki mataki na gaggawa don kaddamar da binciken duniya mai zaman kansa game da mummunan zalunci kan fararen hula a Al-Fashir.

A ranar 26 ga Oktoba, RSF ta ƙwace iko da Al-Fasher, babban birnin Arewacin Darfur, kuma ƙungiyoyi cikin gida da na duniya sun ce an aikata kisan ƙabilanci tare da gargaɗin cewa harin zai iya ƙarfafa rarrabuwar ƙasa ta wurare.

Tun 15 ga Afrilun 2023, sojin Sudan da RSF suke yaƙi a tsakaninsu inda aka kasa yin sulhu zuwa yanzu. Rikicin ya kashe dubban mutane kuma ya tilasta wa miliyoyin yin hijira daga gidajensu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#