A nasa ɓangaren, Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Nijeriya ya bayyana jin daɗinsa kan Allah wadai da harin da gwamnatin Nijeriya ta yi.

Nijeriya ta yi Allah wadai da harin Houthi kan filin jiragen sama na Riyadh a Saudiyya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi Allah wadai da harin da ‘yan Houthi suka kai filin jiragen sama na Sarki Khalid da ke Riyadh a Saudiyya, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Oluwafemi Adeniyi, ya sanya wa hannu, wadda aka wallafa a shafin ma’aikatar na X ranar Lahadi, gwamnatin ta ce tana kallon harin a matsayin keta haƙƙin fararen hula da kuma barazana ga ikon Saudiyya na kare kanta.

Sanarwar ta ce harin na iya kawo cikas ga ƙoƙarin da ake na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Saboda haka, Nijeriya ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, su yi taka-tsantsan, tare da kauce wa matakan da za su iya ƙara rura wutar rikici da kuma jefa rayukan fararen-hula cikin haɗari.

“Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana bayyana goyon bayanta ga gwamnatin da al’ummar Saudiyya, tare da miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin. Haka kuma, tana yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi da wuri,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma yaba wa gwamnatin Saudiyya kan matakan gaggawa da ta ɗauka bayan harin, tare da jaddada amincewar Nijeriya da ƙoƙarin da Saudiyya ke yi na kare tsaron ƙasarta da jin daɗin al’ummarta.

Gwamnatin Nijeriya ta sake jaddada aniyarta ta tallafa wa ƙoƙarin diflomasiyya da tattaunawa domin inganta zaman lafiya da tsaro a duniya. Ta kuma bayyana goyon bayanta ga matakan warware rikice-rikice da kare muhimman ababen more rayuwa a Gabas ta Tsakiya.

A nasa ɓangaren, Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Nijeriya ya bayyana jin daɗinsa kan Allah wadai da harin da gwamnatin Nijeriya ta yi.

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana godiyarsa ga Nijeriya bisa nuna goyon baya da haɗin kai da Saudiyya a kan lamarin.

#