Dollar

43,2789

0.22 %

Euro

50,2002

-0.1 %

Gram Gold

6.375,3800

-0.3 %

Quarter Gold

10.664,4800

0.75 %

Silver

124,3300

-2.65 %

Nijeriya ta samu matsayi na uku bayan ta doke Masar da ci 4-2 a bugun fenareti a gasar AFCON 2025.

Nijeriya ta lashe lambar yabo ta tagulla bayan ta doke Masar a wasan neman matsayi na uku a AFCON

Nijeriya ta lashe lambar yabo ta tagulla bayan ta doke Masar da ci 4-2 a bugun fenareti a wasan neman matsayi na uku a gasar AFCON 2015.

An kammala minti 90 na wasan, wanda aka buga a filin wasa na Mohammed V da ke birnin Casablanca, ba tare da an zura ƙwallo ba.

Hakan ne ya sa aka tafi bugun fenareti. Kuma golan Nijeriya Stanley Nwabali ya nuna jarumta inda ya kaɗe fenareti biyu, ciki har da wanda Mohamed Salah ya buga.

Tawagar Nijeriya ta saka sunan Paul Onuachu wanda ke murza leda a Trabzonspor a cikin ‘yanwasa da ta taka leda da su; hakan ya faru ne bayan ta ajiye fitaccen ɗanwasan Galatasaray Victor Osimhen da na Besiktas Wilfred Ndidi a benci a farkon wasan.

Nijeriya ta ci ƙwallaye biyu ta hannun Paul Onauchu da Ademola Lookman amma lafari bai amince da su ba.

An soke ƙwallon da Onauchu ya zura ne saboda ya naushi ɗanwasan Masar Hamdi Fathy a fuska, inda na’urar VAR ta tabbatar da hakan.

‘Tagulla mai kamar zinare’

A saƙon da ya wallafa bayan kammala wasan, shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya taya ‘yanwasan Super Eagles murna ta lashe lambar yabo ta tagulla.

“Duk da karayar zuciyar da aka yi fama da ita bayan an kaye a hannun Maroko a wasan semi-fainal, tawagarmu ta Super Eagles ta nuna jajircewa, inda ta doke Masar kuma ta sanya mu yin alfahari,” in ji Tinubu.

Ya ƙara da cewa: “Wannan lambar yabo ta tagullar ta yi kama da zinare.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#