Sport
Dollar
43,1493
0.03 %Euro
50,2934
0.08 %Gram Gold
6.309,7800
0.93 %Quarter Gold
10.400,5900
0 %Silver
113,4400
2.48 %Salah na Masar da Osimhen na Nijeriya sun taimaka wa kungiyoyinsu kaiwa ga zagayen dab da ƙarshe na AFCON.
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Masar ta Mohamed Salah ta fitar da masu riƙe da kofin AFCON a yanzu Ivory Coast daga gasar bayan nasarar 3-2 a wasan kwata fainal a ranar Asabar, yayin da Victor Osimhen ya yi fice a lokacin da Nijeriya ta doke Aljeriya 2-0 a yayin da take shirin tunkarar Maroko, mai masaukin baƙi.
A Agadir, wasan zagayen kwata fainal mai cike da tashin hankali ya ga Omar Marmoush da Ramy Rabia sun zura kwallo a rubu’i na farko na wasa ga Masar kafin Ahmed Aboul-Fetouh ya yi kuskuren cin gida inda ya bayar da dama ga Ivory Coast.
Salah ya ci ta uku ga Masar a bayan hutun rabin lokaci kuma suka tsaya kan nasarar duk da cewa Guela Doue ya sake rage gibin.
Masar za ta fafata da Senegal a wasan dab da na karshe a ranar Laraba a Tangier.
"Ina so in gode wa 'yan wasa matuka. Su 'yan Masar ne na gaskiya waɗanda ke fafutukar kawo farin ciki ga mutanensu," in ji mai horarwa Hossam Hassan.
A halin yanzu, Masar ta tabbatar da ƙarfinta a kan Ivory Coast a AFCON tun lokacin da suka fara haɗuwa shekaru 56 da suka wuce. Yanzu Masar ta samu nasara sau 11 a kan Ivory Coast, yayin da Ivory Coast suka yi nasara sau ɗaya kacal.
Mafarkin Salah
Salah ya taimaka wa Liverpool lashe Premier League, FA Cup, League Cup, Champions League da Club World Cup a tsarin ta na baya, amma mafi daraja daga nahiyar Afirka ya kasance abin da bai samu ba.
Dan wasan mai shekaru 33 sau biyu ƙasarsa na zuwa na biyu a gasar ta AFCON bayan rashin nasara a wasan karshe na AFCON da Cameroon a 2017 da kuma Senegal shekaru biyar bayan haka. Hakanan ya kasance cikin kungiyar ƙwallon ƙafar ta Masar a lokacin da aka cire su ba tsammani a matakin sili-ɗaya-ƙwale
Yanzu ya rage masa wasanni biyu kafin ya cika mafarkin sa na dogon lokaci na taimaka wa Masar lashe AFCON karo na takwas domin kafa tarihi.
Salah ya iso Maroko don babban taron wasannin na Afirka cikin rashin tabbas kan makomarsa a Liverpool bayan nuna fushi da ya yi bayan wasan da suka yi da Leeds United.
Amma a AFCON ya nuna kwazon sosai, inda ya zura kwallaye sosai ga Zimbabwe da Afirka ta Kudu a matakin rukuni, sannan kwallon da ta tabbatar da nasara a zagaye na 16 a kan Benin.
Ƙwallon da ya ci a ranar Asabar ita ce ta huɗu da ya ci a gasar.
Kallo ya koma kan Osimhen
Wannan shi ne adadin kwallayen da Osimhen ya ci, wanda ya zura guda ɗaya kuma ya bayar da taimako aka ci ɗaya yayin da Nijeriya ta kawo ƙarshen burin Aljeriya a Marrakesh.
Nijeriya ta karɓe iko da wasan kafin tafiya hutun rabin lokaci kafin ta samu nasarar zura ƙwallo mintuna biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci inda Osimhen ya ci ƙwallon da kai bayan Bruno Onyemaechi ya masa kurosin.
Gwarzon ɗan wasan na Afirka na shekara ta 2023 ya zama kuma wanda ya taimaka domin cin ƙwallo ta biyu kafin minti na 60, inda ya bai wa Akor Adams dama wanda ya zagaya mai tsaron raga ya zura ƙwallon, abin da ya sa Super Eagles suka samu tazara mai wahalar kamowa.
"Ina murna kwarai da gaske ga dukan tawagar saboda irin yadda suka buga wasa mai kyau da tawagar Aljeriya," in ji Osimhen bayan karɓar kyautar mafi kyawun ɗan wasa a wasan.
"A gare ni, kawai na yi aikina. Na yi ƙoƙarin fafutukar samun ƙwallaye ko taimakawa a same su, amma duk tawagar ce ta cancanci yabo."
Nijeriya, wadda ta kasance ta biyu a Gasar AFCON ta baya a Côte d'Ivoire, ta zo Maroko tana ɗauke da zafin rashin samun gurbin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya mai zuwa, amma suna mafarkin lashe kofin nahiyar karo na hudu anan.
‘Nijeriya ta cancanci nasara’
"Maroko kungiya ce mai ƙarfi. Ba abu ne mai sauƙi ba idan ƙsa ta kasance ita ke karɓar baƙunci saboda akwai matsin lamba sosai a tattare da ita," in ji mai horar da Nijeriya Eric Chelle.
"Abin da nake fata shi ne zai kasance wasan ban sha'awa tsakanin ƙungiyoyi biyu masu kyau, kuma ƙungiyar da ta fi cancanta ta yi nasara."
Babban taron magoya bayan su da suke a filin wasa na cike da ƙwarin gwiwa bayan tawagar Vladimir Petkovic ta burge a matakin rukuni kuma ta doke Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo a zagaye na 16.
Sai dai Petkovic ya amince an yi musu rauni sosai; ya ce tawagarsa a wasu lokuta "kamar mai dambe ne da ake naushinsa yana kwance a ƙasa.
"Nijeriya ta ci nasara bisa cancanta. Sun fi mu," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Comments
No comments Yet
Comment