Sanarwar ta Nijeriya na zuwa ne a ranar Litinin, a lokacin da jama’a da dama a fadin yankin ke ta tofa albarkacin bakinsu kan batun, tun bayan da kasashen uku suka sanar da matakin nasu a ranar Lahadi da hantsi.

Nijeriya ta ce ba ta ji dadin ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga ECOWAS ba

Nijeriya ta bayyana rashin jin dadinta kan sanarwar da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi wacce ke nuna cewa kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar din sun janye daga kasancewarsu a Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.

Sanarwar ta Nijeriya na zuwa ne a ranar Litinin, a lokacin da jama’a da dama a fadin yankin ke ta tofa albarkacin bakinsu kan batun, tun bayan da kasashen uku suka sanar da matakin nasu a ranar Lahadi da hantsi.

Kasashen sun ce sun dauki matakin ficewa daga ECOWAS ne saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabar su da ma sauran kalubalen da suke fama da su.

Amma tun da fari ECOWAS ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya wacce ta fitar da sanarwar rashin jin dadin kasar kan matakin makwabtan nata, ta ce “Kusan shekara 50 kenan ECOWAS take aiki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dimokuradiyya a yankin.

“Nijeriya tana tare da ECOWAS don jaddada tsarin da ya dace da kuma kudurinmu na kare da karfafa hakki da jin dadin dukkan 'yan kasashe mambobin kungiyar,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Ambasada Francisca Omayuli.

Ta ci gaba da cewa Nijeriya ta yi aiki da gaskiya da aminci wajen tuntubar dukkan 'yan’uwa na kungiyar ECOWAS don magance matsalolin da muke fuskanta. Yanzu a bayyane yake cewa waɗanda ke neman barin al'ummarmu ba su da irin wannan kyakkyawar aniya.

“Maimakon haka, shugabannin da ba zaɓaɓɓu ba, suna hana jama'arsu 'yancin yin zaɓi na asali game da 'yancin yin tafiya da 'yancin yin kasuwanci da ƴancin zaɓar shugabanninsu."

Sai dai Nijeriya ta ce kofarta a bude take don tattaunawa da Burkina Faso da Mali da Nijar ta yadda al’ummomin yankin za su ci gaba da jin daɗi da cin moriyar tattalin arziki da ƙimar dimokradiyya da kungiyar ECOWAS ta amince da su.

Ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya da zu ci gaba da ba da goyon bayansu ga ECOWAS da kuma hadin kai.

#