Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Gwamnatin Nijar ta bayar da wa'adin 31 ga Mayun 2025 ga duka ma’aikatan su fice daga ƙasar, kamar yadda wata wasiƙa da Ministan Man Fetur na Nijar Dakta Sahabi Dumarou ya aika wa kamfanin ta nuna.
Ministan Man Fetur na Nijar Dakta Sahabi Dumarou ya bayar da umarni ga kamfanin man fetur na CNPC ya kori duka ma’aikata ‘yan ƙasashen waje da ke aiki a kamfanin nan take waɗanda suka shafe fiye da shekara huɗu suna aiki a kamfanin.
Ministan ya bayyana haka ne a wata wasiƙa da ya aika ga shugaban kamfanin mai na CNPC inda ya bayar da wa’adin 31 ga Mayun 2025 ga duka ma’aikatan su fice daga ƙasar.
Ministan ya zargi kamfanin na China da “raina” dokokin Nijar musamman doka mai lamba 2024-34 wadda aka yi a Agustan 2024 wadda ke da alaƙa da haƙo mai da kuma doka mai lamba 2012-45 wadda aka yi a 25 ga Satumbar 2012 kan tsarin aiki.
Wannan matakin na daga cikin yunƙurin da gwamnatin ta Nijar ke yi na ƙwace iko da ma’adinan ƙasar da kuma samar da ayyuka ga ‘yan ƙasar.
Gwamnatin ta Nijar na zargin kamfanonin ƙasashen waje da dama daga ciki har da CNPC kan yadda ma’aikatansu na ƙasashen waje ke yin kaka-gida a manyan muƙamai da hana ‘yan ƙasa samun gurbi, wanda hakan ya saɓa wa gwamnatin ta Nijar.
Ko a watan Maris ɗin da ya gabata, sai da gwamnatin ta Nijar ta sallami manyan shugabannin kamfanin mai na ƙasar China uku kan rashin daidaito a albashi tsakanin ‘yan ƙasa da kuma baƙi.
Haka kuma gwamnatin ta ɗauki matakin sauya fasalin wasu dokoki waɗanda za su ba ‘yan Nijar damar sa hannun jari a kamfanonin WAPCO da kuma dama da ‘yancin yin aiki a kamfanin CNPC daidai da yadda ‘yan China ke da ‘yanci.
Comments
No comments Yet
Comment