Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ƙungiyar Likitoci ta Sudan ta ce ana ci gaba da aikin ceto sakamakon akwai gomman masu haƙar zinarin da har yanzu suke ƙarƙashin ɓaraguzai.
Mutum shida sun rasu inda 12 kuma suka jikkata, wasu gommai kuma har yanzu ba a gansu ba bayan wani wurin haar zinari ya rufta a Jihar Kordofan ta Kudu da ke kudancin Sudan, kamar yadda ƙungiyar likitoci ta Sudan ta tabbatar a ranar Juma’a da dare.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar agajin ta likitoci ta fitar ta ce: "Ruftarwar wurin haƙar zinari a Abu Jubaiha ya yi sanadin mutuwar mutum shida kuma mutu 12 sun jikkata. Akwai gomman mutane da ba a san halin da suke ciki ba sakamakon sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai a lokacin fitar da sanarwar."
Ƙungiyar ta yi kira da a ƙara kaimi a ayyukan ceto da kuma samar da taimakon gaggawa ga waɗanda suka ji jikkata.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta ɗauki matakai don kare masu haƙar ma’adinai, ciki har da saka dokoki na bayar da kariya, horaswa, da kuma saka musu ido akai-akai, don hana afkuwar irin waɗannan masifu.
Ta jaddada cewa sakaci na cibiyoyi da rashin aiwatar da dokoki na jefa rayukan masu haƙr ama’adinan a cikin hatsari.
Ƙungiyar likitocin ta kuma yi kira da a ɗauki matakin kama waɗanda ke da alhakin faruwar lamarin da kuma aiwatar da matakai na zahiri don hana maimaita irin waɗannan abubuwa.
Samar da Ayyuka
Aikin haƙar zinari na masu ƙaramin ƙarfi na bai wa fiye da mutum miliyan biyu aiki a faɗin Sudan, akasari inda suke ayyukan a cikin mawuyacin yanayi, kuma yana samar da kusan kashi 80 cikin 100 na jumullar zinari a ƙasar.
Duk da cewa gwamnatin Sudan ba ta haramta haƙar zinari n masu ƙaramin ƙarfi ba, amma tana ƙoƙarin saka tsari a harkar da kuma a ido. Duk da cewa akwai matsaloli, amma wannan ɓangaren yana ba da aikin yi ga mutane da yawa na Sudan.
Sudan ta dogara da zinari a matsayin babban tushen samun kuɗin waje bayan ta rasa kusan uku cikin huɗu na kuɗaɗen mai bayan ɓallewar Sudan ta Kudu a 2011, lamarin da ya kuma haifar da rasa kusan kashi 80 na ajiyar kudin ƙasashen waje na ƙasar.
Comments
No comments Yet
Comment