Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban gwamnatin da ke mulkin Sudan Abdel Fattah al Burhan ya ce ƙasarsa ta amince Turkiyya ko Qatar su kasance masu shiga tsakani, amma RSF ta yi watsi da matakin.

Ba za a samu zaman lafiya a Sudan ba sai an kawar da RSF — Burhan

Ba za a taɓa samun zaman lafiya a Sudan ba sai an kawar da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF), a cewar shugaban gwamnatin ƙasar Abdel Fattah al Burhan.

Da yake magana da ‘yanjarida a gidansa da ke Port Sudan ranar Lahadi, Burhan ya ce, "Ba za a samu zaman lafiya ba sai an kawar da RSF, kuma duk wata tattaunawar zaman lafiya da aka sanya RSF a cikinta, za ta jinkirta rikici ne kawai. Hanya ɗaya ta samun dauwamammen zaman lafiya ita ce a kawar da RSF. Hakan ba ya nufin dole dukka su mutu; yana nufin su miƙa makamansu tare da yin saranda."

Burhan ya ƙara da cewa yaƙin da ake yi a ƙasar ya haddasa gagarumar ɓarna, wadda ta shafi fararen-hula da kuma gine-gine a faɗin ƙasar.

Ya ce babu wani ɗan ƙasar Sudan da yaƙin bai shafe shi ba amma duk da haka al’umar ƙasar sun haɗa kai wajen yaƙar ƙungiyar da ke tayar da ƙayar baya.

Yayin da yake magana kan ƙoƙarin ƙasashen duniya na wanzar da zaman lafiya, ya nuna ƙarin kiraye-kiraye da suke yi kan hakan bayan RSF ta ƙwace yankin Al Fasher a watan Oktoba, yana mai cewa matakin na zuwa ne a yayin da ake neman ganin rundunar ta faɗaɗa ikonta zuwa wasu yankuna.

"An bayar da shawarar tsagaita wuta yayin da aka mamaye Al Fasher," in ji shi. "Bayan an ƙwace yankin, an samu ƙaruwar waɗannan kiraye-kiraye saboda suna so RSF ta karɓe iko da ƙarin yankuna."

RSF ta yi watsi da buƙatar masu son shiga tsakani

Burhan ya ce ƙasarsa ta amince Turkiyya ko Qatar su kasance masu shiga tsakani, amma RSF ta yi watsi da buƙatar. Ya ƙara da cewa su ma ƙasashen da ke yankin irin su Saudiyya da Masar suna iya taka rawa kan lamarin.

"Da farko, mun yi imani da Allah, sannan mun amince da (shugaban Turkiyya Recep Tayyip) Erdogan," in ji shi.

Kazalika ya jaddada cewa dakarun RSF da sojojin Sudan ba ƙarfi iri ɗaya gare su ba.

"Ɓangarori biyu da ke faɗa da juna ba ƙarfi iri ɗaya gare su ba. RSF ba daidai take da sojojin Sudan. Duka duniya tana faɗin wannan," a cewarsa.

Duk da matakan MDD, RSF ta ci gaba da kai hare-hare tare da shigar da makamai cikin Sudan, musamman zuwa yankin Darfur ba tare da fuskantar hukunci ba, in ji Burhan.

"A matsayinmu na al’ummar Sudan da kuma rundunar soji, mun sha alwashi sai mun kawar da RSF. A shirye muke mu amince da duk wata hanya ta samun zaman lafiya," a cewarsa.

Sojojin Sudan da dakarun RSF sun ƙaddamar da yaƙin basasa tun watan Afrilun 2023 bayan sun soma rikici game da haɗa dakarun RSF da rundunar sojin ƙasar a wuri guda.

Yaƙin ya haddasa matsalar jinƙai mafi muni a duniya, tare da yin sanadin mutuwar dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#