Ya ƙara da cewa gidaje 12,985 ne suka rufta sakamakon ambaliyar yayin da dabbobi 1,366 suka salwanta.

Mutum 81 sun mutu a jerin ambaliyar ruwa da suka shafi mutum 97,334 a shekarar 2026 a Nijar

Jerin ambaliyar ruwa sun kashe mutum 81 da jikkata mutum 131 tare da shafar mutum 97,334 a cikin bala’o’in da suka shafi iyalai 13,976 a Nijar ya zuwa ranar 31 ga watan Oktoban 2026, kamar yadda Ministan Adadin Jama’a da Matakan Zamantakewa, Sani Douda, ya bayyana.

Kamfanin Dillancin labaran Nijar (ANP) ya ba da rahoton cewa an bayyana wannan ne a wajen buɗe taron nazari kan yadda aka tafiyar da ambaliya ta shekarar 2026 a Maradi ranar Talata.

Taron wanda aka yi a ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Maradi region, Sufeto Janar na ‘Yansanda Issoufou Mamane, a ɗakin taron otel ɗin Guest House, an yi shi ne don nazari kan matakan da aka ɗauka a cikin shekarar don gano gazawa da kuma gabatar da sahwarwari don inganta hana aukuwar ambaliya da kuma magance ta a shekarar 2027, in ji ANP.

A nasa jawabin, gwamnan Jihar Maradi ya yaba wa jajircewar hukumomi a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani da kuma Firayim Minista Ali Mahaman Lamine Zeine, wajen inganta yanayin rayuwar jama’a da ƙuma ƙarfafa juriyarsu a gaban masifun yanayi.

Ya jaddada muhimmancin yin taron bitan kuma ya bayyana gamuswarsa da zaɓar Jihar Maraɗi a matsayin mai karɓar baƙuncin tarukan.

Da yake magana a madadin MInistan Jama’a da Haɗin Kan ƙasa, Sani Douda ya bayyana cewa adadin waɗanda ambaliya ta kashe zuwa ranar 31 ga watan Oktoba sun kai mutum 81, inda ambaliya ta shafi iyalai 13,976 tare da shafar mutum 97,334 da lkuma jikkata mutum 131.

Ya ƙara da cewa gidaje 12,985 ne suka rufta sakamakon ambaliyar yayin da dabbobi 1,366 suka salwanta.

Ya jaddada cewa ƙoƙarin da aka yi a cikin shekarar sun mayar da hankali ne kan ƙarfafa sa ido da kuma tsare-tsaren ba da gargaɗi da wuri da shirin aiki da wayar da kan jama’a.

Sani Douda ya bayyana cewa nazarin zai ba da damar tunanin kan matakan da aka ɗauka da gano kurakurai da da kuma koyon darrusa masu muhimmanci wajen inganta hana aukuwar ambaliya da tafiyar da ambaliya a shekarar 2027.

Daga bisani, ya yi kira ga mahalarta taron su b ada shawarwari masu ɗorewa don ƙarfafa hana aukuwar masifu da tsare-tsaren tafiyar da lammura.

A nasa ɓangaren, wakilin WFP Ofishin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), shugaban ma’aikatan WFP a Nijar, Gaspard Cirhalwirwa, ya yaba wa ƙoƙrin gwamnatin Nijar tare da jajircewar hukumomi da al’ummomi da masu ruwa da tsaki wajen hana aukuwar masifu da magance su.

Ya bayyana cewa wannan taron bitar aikin wata dama ce ta koyan darrusa daga yadda aka tafiyar ambaliya ta shekarar 2026 don ƙarfafa yadda za a tunkari shekarar 2027.

Gaspard Cirhalwirwa ya sake jaddada jaircewar WFP ga tallafa wa gwamnatin Nijar wajen hana aukuwar masifu da magance su, musamman ta hanyar ƙrfafa tsare-tsaren ƙasa da ikon shiri da juriyar al’umma.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: ANP

#