Adadin ya ɗara ninki cikin shekara shida, kamar yadda hukumar kula da ‘yan guduna hijira ta MƊƊ (UNHCR) ta bayyana ranar Jumma’a. Adadin ya haɗa da ‘yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa 818,000, in ji ta.

MƊD: An raba mutane miliyan huɗu da gidajensu a Burkina Faso da Mali da Nijar

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta nuna damuwa game da matsalar raba mutane da gidajensu a tsakiyar yankin Sahel inda aka tilasta wa kusan mutum miliyan huɗu tserewa daga gidajensu a Burkina Faso da Mali da kuma Nijar.
Adadin ya ɗara ninki cikin shekara shida, kamar yadda hukumar kula da ‘yan guduna hijira ta MƊƊ (UNHCR) ta bayyana ranar Jumma’a. Adadin ya haɗa da ‘yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa 818,000, in ji ta.
"Matsalar na tsananta ne sakamakon ci-gaba da kai hare-haren da ke shafar fararen hula da matsalar sauyin yanayi da gagarumar raguwar kuɗin jinƙai," in ji sanarwar hukumar UNHCR ɗin.
A shekarar 2020, hukumar UNHCR ta ce yankin ya ƙirga fiye da mutum miliyan 1.7 da aka raba da gidajensu a cikin ƙasashensu da kuma ‘yan gudun hijira 365,000.
Hankalin ƙasashen duniya na ‘ja da baya'
"Tare, waɗanna matsin suna tilasta wa ƙarin iyalai su tsere, lamarin da ke ƙarar da hanyar samun kuɗin shiga da kuma taƙaita damarmaki wa waɗanda aka raba da gidajensu su sake gina rayuwarsu, abin da ke ba da gudumowa ga ƙarin hijira a ciki da wajen yankin ," kamar yadda Abdouraouf Gnon-Konde, daraktan yankin yammaci da tsakiyar Afirka a hukumar UNHCR ya bayyana.
"Abin taƙaici, hankalin duniya na ja da baya," kamar yadda ya bayyana a Geneva, bayan ya kai ziyara a yankin.
Gnon-Konde ya ƙara da cewa rashin tsaro yana ƙara matsi kan tsarin neman mafaka. A ƙasar Mali, yawancin ‘yan gudun hijira sun zo ne daga ƙasar Burkina Faso mai maƙwabtaka.
Hukumar UNHCR ta ce Koro, a yankin Bandiagara na tsakiyar Mali kusa da kan iyaka da Burkina Faso, na ɗauke da ‘yan gudun hijiran Burkina Faso 86,000 – ciki har da fiye da ƙananan yara 14,000 – a watan Yuli, bayan kwararowar da suka yi kwanan nan.

An yi rijistar ƙarin waɗanda aka raba da gidajensu

Hukumar ta MƊD ta ce adadin ‘yan gudun hijira a yankin ya kusan kai yawan mutane da ke cikin gundumar, lamarin da ke ƙara matsi kan taƙaitaccen fili da ruwa da kuma yi wa ayyukan jinya yawa.

Ta yi gargaɗin cewa matsalar na ƙara bazuwa har wajen yankin Sahel, inda ɗaruruwan dubban mutane da aka raba da gidajensu ke zuwa a bakin tekun Yammacin Afirka, ciki har da Benin da Côte d'Ivoire da Ghana da kuma Togo. Amma hukumar UNHCR na fuskantar tsananin gazawa na kuɗi. A watan Satumba, ta yi kiyasin cewa ta karɓi kashi 27 cikin 100 ne kawai na kuɗin da ake buƙata wajen ɗaukar nauyin aikinta a yankin Sahel.

#