Sport
Dollar
40,9411
0.09 %Euro
47,9607
0.44 %Gram Gold
4.383,8900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Bayan Crystal Palace ta doke Liverpool a wasan cin kofin Charity Shield, yau ta tashi da jimamin rashin nasara a ƙarar da ta kai hukumar UEFA game da hana ta buga gasar Europa ta baɗi.
A maraicen Lahadi 10 ga Agusta Crystal Palace ta doke Liverpool a bugun ɗurme, inda ta ɗaga kofin Charity Shield na Ingila, wanda ake bugawa tsakanin zakarun gasannin Firimiya da na FA.
Yayin da Crystal Palace ke murnar wannan nasara ta biyu a shekarar nan, a yau kuma ƙungiyar ta shiga baƙin cikin rashin nasara a ɗaukaka ƙarar da ta kai hukumar UEFA game da korar ta daga gasar Europa ta baɗi.
Kotun Sulhu ta Wasanni ta yi hukuncin kan ɗaukaka ƙarar da Palace ta yi game da hana ta buga gasa ta biyu mafi girma a Turai, Europa.
A yanzu Crystal Palace za ta buga gasar Turai ta uku a daraja, ta Conference kamar yadda hukumar ƙwallo ta Turai UEFA ta yanke tun da fari.
Sakamakon hukuncin, Nottingham Forest za ta maye gurbin Palace, saboda ta ƙare kakar bara a mataki na 7 a teburin Firimiya.
Wannan hukunci zai janyo wa Palace asara saboda za ta iya rasa fam miliyan £20 na kuɗin lashe gasa.
Comments
No comments Yet
Comment