Hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta gudanar da bincike kan kisan da Isra'ila ta aikata a Gaza, lamarin da ke kara fargaba kan yiwuwar aikata ''laifukan yaki.''

Kashe-kashe da Isra'ila ke aikatawa a Gaza na iya zama 'laifin yaki' - MDD

An samu rahotanni masu ban tsoro da ke zargin rundunar tsaron Isra'ila IDF da kashe Falasdinawa akalla 11 a yankin Al Remal da ke makwabtaka da Birnin Gaza, a cewar wani rahoto da ofishin hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinu da aka mamaye OHCHR OPT ya fitar.

Lamarin wanda ya auku a gaban 'yan uwan mutanen da aka kashe, ''ya haifar da damuwa tare da sanya firgici game da yiwuwar aikata ''laifin yaki"

Wadannan zarge-zargen sun biyo bayan ikirarin da ke nuni da cewa sojojin Isra'ila na kai hari tare da kashe fararen-hula, a cewar sanarwar.

La'akari da wadannan munanan zarge-zarge, hukumar OHCHR OPT ta bukaci hukumomin Isra'ila da su gaggauta kaddamar da wani sahihin bincike mai zaman kansa, kuma Idan har zarge-zargen suka tabbata, ya zama wajibi a hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata laifin.

Kazalika hukumar ta ce, dole a dauki matakai da za su hana sake faruwar irin wadannan munanan laifuka sannan akwai bukatar sa ido sosai a lokutan rikici.

OHCHR ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Disamba, 2023, tsakanin karfe tara zuwa 11 na dare, lokacin da sojojin Isra'ila suka yi wa ginin Al Awda da aka fi sani da ginin Annan a yankin Al Remal da ke makwabtaka da birnin kawanya tare da kai farmaki cikinsa.

A cewar rahoton, ginin ya kasance matsuguni ga iyalai uku.

A bayanan da shaidu da majiyoyin yada labarai da kuma kungiyar kare hakkin bil'adama ta ''Euro-Med Human Rights'' suka rawaito, sun ce an ga yadda sojojin Isra'ila suka mamaye ginin inda suka raba maza da mata da yara sannan suka yi ta harbi har suka kashe akalla mutum 11.

Akasarin mutanen da aka kashe a gaban 'yan'uwansu 'yan shekaru sama da 20 ne zuwa 30.

#