Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170.

KAI-TSAYE: Yara a Gaza sun yi zanga-zangar adawa da mamayar Isra'ila ta hana su abinci da ruwa

0230 GMT — Yaran Gaza sun yi zanga-zangar adawa da mamayar Isra'ila ta hana su abinci da ruwa

Yara Falasdinawa da dama a birnin Gaza da ke arewacin yankin Gaza sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ƙarancin abinci da ruwan sha a ƙarƙashin mamayar da Isra'ila ke yi.

Yaran sun yi tattaki ne a ranar Talata a titunan birnin Gaza riƙe da tutoci ɗauke da rubuce-rubucen "burudi ne mafarkina a kullum" da kuma "muna son abinci," da dai sauransu.

Riƙe tukwanen da babu komai a ciki a lokacin gangamin nuna rashin abincin, yaran sun yi ta ihun neman rayuwa mai kyau.

"Muna mutuwa da yunwa, ba mu da abin da za mu ci, ana tilasta mana cin abincin dabbobi," Ayat Ashour 'yar shekara 10 ta shaida wa Anadolu.

Ta ƙara da cewa "Ba ma iya samun abinci, muna so mu rayu, muna son agajin abinci. ... Mutanen arewacin Gaza ba sa samun abin da za su ci, babu madara ga yara," in ji ta.

Wani yaro Omar al Shenbari, mai shekara 14, ya ce: "Muna tafiya ne domin mu ɗaga muryarmu ga duniya cewa muna son mu ci burodi, babu abinci ko ruwa (a Gaza)."

"Sau ɗaya muke cin abinci a rana kuma shi ma ba ya ƙosar da mu, galibi ruwa ne da tumatir," in ji Omar.

A ƙarshe ya aike da saƙo zuwa ga duniya yana mai cewa: "Muna cikin mawuyacin hali, dole ne ƙasashen Larabawa da ma duniya baki ɗaya su tsaya tare da mu."

0144 GMT — Isra’ila ta sanar da shirin kayyade adadin masu zuwa Sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa

Isra’ila ta sanar da cewa za ta kayyade adadin Musulman da za su rinƙa zuwa Sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa a lokacin watan Ramadana

Isra’ila ta sanar da cewa za ta kayyade adadin Musulman da za su rinƙa zuwa Sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa a lokacin watan Ramadana.

Ministan ƴan sandan ƙasar ne ya sanar da hakan inda ya ce akwai yiwuwar masallacin ya kasance wurin da za a gudanar da zanga-zanga.

Ministan tsaron ƙasar Itamar Ben-Gvir a ranar Talata ya ce yunƙurin da ya yi na haramta wa akasarin Musulmai Sallar Juma’a hakan bai yiwu ba sakamakon Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da hakan.

Sai dai ya ce duk da hakan za a ƙayyade adadin mutanen zuwa mutum 40,000 ko 50,000.

0947 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa shida da safiyar Laraba

Aƙalla Falasɗinawa shida aka kashe a safiyar Laraba sakamakon hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wata mota a birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa wani jirgin yaƙin Isra’ila ya kai hari kan wata motar farar hula da ke wucewa kan titin “Abu Hosni” da ke tsakiyar Deir al-Balah.

A halin da ake ciki kuma, wakilin Anadolu ya kara da cewa tun da sanyin safiyar Larabar nan ne sojojin Isra'ila suka yi ta luguden wuta a yankunan gabashin Deir al-Balah.

1152 GMT — An kashe sojin Isra'ila ɗaya an ji wa uku 'mummunan rauni'

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta ce wani sojanta ya rasa ransa sakamakon raunin da ya ji a yayin arangama da dakarun Falasɗinawa a arewacin Gaza.

A wata sanarwa da ya fitar, rundunar sojin ta Isra’ila ta ce sunan sojan Staff Sgt. Avraham Wovagen mai shekara 21.

A wani lamari na daban kuma, wasu sojoji biyu sun samu rauni mai tsanani bayan wani makamin roka ya faɗa musu a Gaza.

Haka kuma sanarwar ta ce akwai wani soja na uku da aka raunata a yayin wata arangama a kudancin Zirin Gaza.

0215 GMT — Asibitin Nasser na Gaza ya zamo dandalin mutuwa — MDD

Wani jami'in ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, OCHA ya bayyana damuwarsa kan halin da Asibitin Nasser ke ciki a birnin Khan Younis a kudancin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

"Yanayin da ake ciki yana da ban tsoro. Akwai gawawwaki a barbaje a kan hanyoyi. Marasa lafiya na cikin mawuyacin hali," in ji Jonathan Whittall, babban jami'in kula da ayyukan jinƙai na OCHA a yankin Falasɗinawa da aka mamaye.

Ya ƙara da cewa "Wannan waje ya zamo dandalin mutuwa, ba wajen warkar da marasa lafiya ba."

0311 GMT — Isra'ila ta kai hari matsugunin ƙungiyar likitocin MSF a Gaza

Isra'ila ta kai hari a wani matsugunin ƙungiyar agaji ta Doctors Without Borders (MSF) a Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ta kashe aƙalla mutane biyu.

"A daren yau, sojojin Isra'ila sun kai wani samame a Al Mawasi, Khan Younis a Gaza, inda aka harba makamai wani matsuguni da ke karɓar baƙuncin ma'aikatan MSF da iyalansu," in ji MSF a shafin X.

“Yayin da ake ci gaba da samun cikakken bayani, yanzu haka ma’aikatan motar daukar marasa lafiya sun isa wurin, inda aka kashe akalla ‘yan'uwan abokan aikinmu biyu tare da mutane shida da suka ji rauni. Mun firgita da abin da ya faru,” in ji sanarwar.

0100 GMT — Amurka da Rasha za su yi magana kan mamayar Isra'ila a babbar kotun MDD

A ranar Laraba ne Amurka da Rasha za su gabatar da muhawara a shari'ar da ake yi a Kotun Ƙolin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke nazarin halaccin mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinu.

Fiye da ƙasashe 50 ne za su gabatar da muhawara har zuwa ranar 26 ga watan Fabrairu. An kuma shirya Masar da Faransa su yi magana ranar Laraba.

A ranar Talata, ƙasashe 10 ciki har da Afirka ta Kudu, sun yi kakkausar suka ga yadda Isra'ila ke gudanar da ayyukanta a yankunan da ta mamaye, inda da dama suka buƙaci kotun da ta ayyana mamayar a matsayin haramtacciya.

#