Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 207 - ya kashe Falasdinawa akalla 34,488 tare da raunata wasu 77,643 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki.

Kai-tsaye: 'Yan Houthi sun yi ikirarin kai hari kan jiragen ruwa huɗu, ciki har da na Amurka biyu

2115 GMT — 'Yan Houthi sun yi ikirarin kai hari kan jiragen ruwa 4, ciki har da na Amurka biyu

Kakakin rundunar Houthi Yahya Sarea ya bayyana a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin cewa 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun kai hari kan jiragen ruwa guda biyu na Amurka da kuma jirgin CYCLADES a Bahar Maliya da kuma MSC Orion da ke gabar Tekun Indiya.

"Dakarun Yemen sun kai farmakin soji kan jiragen ruwan yaƙi da suke mana barazana a Bahar Maliya, inda harin na jirage marasa matuƙa ya sauka a kan jiragen yaƙin Amurka guda biyu. An cimma nasara a manufofin sojin," in ji Sarea.

"Harin da aka kai wa jirgin ya zo ne bayan da ya karya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa tasoshin ruwa na Falasdinu da aka mamaye, a kan hanyarsa ta zuwa tashar jiragen ruwa ta Umm al-Rashrash a ranar 21 ga Afrilu, inda ya yi amfani da salon yaudara da cewa yana kan hanyarsa ta zuwa wata tashar ruwan ne daban," in ji shi.

Sojojin Houthi sun kwashe tsawon watanni suna kai hare-hare kan hanyoyin jiragen ruwa domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa na Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kashe-kashe a Gaza.

2134 GMT — Tawagar Hamas za ta koma birnin Alkahira da amsa kan batun sulhu

Wata tawaga ta Hamas ta bar Masar bayan tattaunawa kan yiwuwar sasantawa da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su, kuma za ta dawo amsa kan sabuwar buƙatar, kamar yadda wata kafar yada labarai da ke goyon bayan Gaza ta sanar a ranar Litinin da daddare.

A cewar majiyoyin Masar din da Al-Qahera News ta rawaito da kuma wani shafin da ke da alaka da hukumar leken asirin Masar, sun ce tawagar Hamas ta bar birnin Alkahira, kuma za ta dawo da amsa a rubuce kan ƙudirin sulhun.

#