Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 214, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,735 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,108 ne suka jikkata.

Kai-tsaye: Tankokin yaƙin Isra'ila sun shiga kudancin birnin Rafah na Gaza — Rahoto

2248 GMT — Tankokin yaƙin Isra'ila sun shiga kudancin birnin Rafah na Gaza — Rahoto

Tankokin yakin Isra'ila sun shiga birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, inda suka kai kusan mita 200 daga tsallaken Masar, kamar yadda wani jami'in tsaron Falasdinu da wani jami'in Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Jami'in na Masar ya ce da alama "aikin" yana da iyaka. Shi da tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Hamas sun ce jami'an Isra'ila sun sanar da Misirawan cewa dakarunsu za su janye bayan kammala aikin.

Jami'in na Masar da ke yankin Rafah na kasar Masar da kuma jami'in tsaron Falasdinawa sun yi magana ne da manema labarai.

Tun da farko a ranar Litinin, Majalisar Ministocin Yakin Isra'ila ta yanke shawarar ci gaba da kai farmakin soji a Rafah, bayan da kungiyar Hamas ta sanar da amincewa da shawarar Masar da Qatar na cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

2300 GMT — Turkiyya na fatan Isra'ila ta ɗauki irin matakin Hamas na amincewa da tsagaita wuta

Turkiyya ta yi marhabin da shawarar tsagaita wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta sanar da cewa ta amince da ita, inda ta kara da cewa tana sa ran Isra'ila ta ɗauki irin wannan mataki, in ji Shugaba Recep Erdogan.

"Muna maraba da sanarwar Hamas cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tare da kokarinmu, kuma ya kamata Isra'ila ta dauki matakin da ya kamata," in ji Recep Tayyip Erdogan a ranar Litinin bayan taron majalisar ministocin.

Erdogan ya kuma bukaci "masu ruwa da tsaki na Yammacin Duniya" da su matsa wa gwamnatin Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Turkiyya ta sha matsa ƙaimi kan tsagaita a Gaza tun farkon rikicin watanni bakwai da suka gabata, kuma ta yi kira ga dukkan kasashen duniya da su taimaka wajen ganin an cimma matsaya.

2238 GMT — Isra'ila ta kashe akalla mutane biyar a harin Rafah

Isra'ila ta kashe akalla mutane biyar bayan da ta kai hari a Rafah, in ji wani asibiti a yankin, yayin da Isra'ila ta sha alwashin kaddamar da wani gagarumin farmaki a can.

Asibitin Kuwaiti na birnin ya ce ya karbi "Shahidai biyar da waɗanda suka jikkata da dama" bayan harin da Isra'ila ta kai.

A halin yanzu yankin ya kasance wurin da sojojin Isra'ila ke kai hare-hare kamar yadda shaidu da majiyoyin tsaron Falasdinawan suka bayyana.

#