Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 410 a yau — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 43,922 tare da jikkata fiye da mutum 103,898. A  Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,516 tun daga watan Oktoban 2023.

Kai-tsaye: Shugabannin ƙasashen G20 sun yi kira a aiwatar da 'gagarumin' shirin tsagaita wuta a Gaza da Lebanon

Talata, 19 ga watan Nuwamba, 2024

0021 GMT –– Shugabannin ƙasashe na ƙungiyar G20 sun yi kira a aiwatar da "gagarumin" shirin tsagaita wuta a Gaza da Lebanon a wata sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar a wurin taronsu a Brazil ranar Litinin.

Shugabannin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki na duniya sun yi kira a aiwatar da shawarwarin Amurka na daina buɗe wuta a yankin Gaza na Falasɗinu tare da sakin mutanen da ake garkuwa da su, da kuma tsagaita wuta a Lebanon “da za ta bai wa mutane damar komawa gidajensu cikin salama a dukkan ɓangarorin Blue Line.”

Ƙarin labarai ????

2300 GMT –– An sace kayan abinci daga cikin motocin agaji kusan 100 a Gaza: MDD

An sace abincin da ke cikin motoci kusan 100 da ke ɗauke da kayan agaji da za a kai wa Falasɗinawa ranar 16 ga watan Nuwamba a wani mataki da ake gani yana cikin sata mafi muni a watanni 13 da aka kwashe ana yaƙi a yankin, inda yunwa take ƙara ƙamari, kamar yadda hukumomi biyu na MDD suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin.

Isra'ila ce ta umarci tawagar da ke ɗauke da kayan abincin ta hukumar UNRWA da Shirin Samar da Abinci na MDD su fice daga yankin ba tare da ɓata lokaci ba, sannan ta tilasta musu bi ta hanyar da ba a saba bi ba, wato hanyar Karem Abu Salem, a cewar Louise Wateridge, wata babbar jami'a ta UNRWA.

Ta ƙara da cewa an sace kayan abinci daga cikin motoci casa'in da takwas cikin motoci 109 da ke tawagar kuma an jikkata wasu daga cikin direbobinsu, ko da yake ba ta yi ƙarin bayani kan waɗanda suka kai musu harin ba.

"Wannan lamari ya nuna girman ƙalubalen da muke fuskanta wajen kai agaji a kudanci da tsakiyar Gaza," kamar yadda ta shaida wa Reuters.

#