Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 18 — bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 47,500 tare da jikkata fiye da 61,700 a hare-haren kisan ƙare-dangin da ta kwashe watanni goma sha biyar tana kai wa a yankin.
Laraba, 5 ga Fabrairu, 2025
0219 GMT — Saudiyya ta jaddada cewa ba za ta ƙulla wata alaƙa da Isra'ila ba muddin ba a kafa ƙasar Falasɗinu ba mai cin gashin kanta ba, sannan ta yi watsi da iƙirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa mahukunta a Riyadh sun sassauta matsayarsu.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fitar da wata sanarwa da ke jaddada masayar masarautar ta "yin tsayin-daka ba tare da shayin kowa ba" bayan iƙirarin da Trump yayin ganawarsa a Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Fadar White House.
A lokacin da aka tambaye shi kan ko Saudiyya ta buƙaci kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, Trump, wanda ke aune tare da Netanyahu a Fadar shugaban ƙasa ya ce: "A'a, ba su yi hakan ba."
"Ma'aikatar Harkokin Waje tana jaddada matsayar Masarautar Saudiyya ta kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta ba tare da shayin kowa ba", in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
"Mai Girma Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, Yarima Mai Jiran Gadon Sarauta kuma Firaminista, ya bayyana matsayarmu ƙarara kuma ba tare da tsoro ba a jawabin da ya gabatar na buɗe taron Majalaisar Shura karo na tara ranar 18 ga watan Satumba, 2024."
Sanarwar ta ƙara da cewa yarima ya sake jaddada matsayar masarauta a lokacin taron Ƙasashen Larabawa da Musulmai a Riyadh ranar 11 ga watan Nuwamban 2024, inda ya nanata buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu mai iyaka kamar yadda take a 1967 da kuma kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila take yi wa yankin Falasɗinu.
"Masarautar Saudiyya tana sake jaddada goyon bayanta kuma ba za ta sauya matsayarta ba komai zai faru kuwa.