Isra'ila ta kwashe kwana 265 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,718 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,377, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500.

Kai-tsaye: Ministan Tsaron Isra'ila Gallant ya yi barazanar mayar da Lebanon zuwa "Zamanin Dutse"

0023 GMT — Ministan Tsaron Isra'ila Gallant ya yi barazanar mayar da Lebanon zuwa "Zamanin Dutse"

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant a wata ziyara da ya kai birnin Washington ya bayyana cewa sojojin Isra'ila suna da ikon mayar da kasar Lebanon "komawa zamanin dutse" a duk wani yaƙi da za ta yi da kungiyar Hizbullah, amma ya dage cewa gwamnatinsa ta fi son a samar da hanyar diflomasiyya a kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

Da yake zantawa da manema labarai, Gallant ya kuma ce ya tattauna da manyan jami'an Amurka "kwana daya bayan" shawarwarin da ya gabatar na gudanar da mulki bayan kammala yaƙin Gaza, wanda zai hada da Falasdinawa na gida da abokan hulɗa na yanki da kuma Amurka, amma hakan zai kasance "tsari mai tsawo da sarƙaƙiya. "

2200 GMT — Isra’ila ta kashe mutum biyu a Syria, ta raunata biyar a Lebanon

Isra'ila ta kashe mutane biyu tare da raunata wani soja daya bayan da ta kai hari a kudancin Syria, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnatin Syria suka rawaito.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin ƙasar, SANA ya rawaito cewa an kai hare-hare a wurare da dama a kudancin Syria, lamarin da ya haifar da ɓarna a yankin Tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye, ba tare da bayar da karin bayani kan inda aka kai hare-hare da ɓarnar da aka yi ba.

A kasar Labanon, Isra'ila ta raunata mutane biyar bayan ta kai hari kan wani bene mai hawa biyu a garin Nabatiyeh da ke kudancin kasar Lebanon, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta rawaito.

2200 GMT — Majalisar Dinkin Duniya ta kasa amfani da hanyar da Isra'ila ta amince a bi wajen isar da agaji

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta iya yin amfani da hanya daya tilo da Isra'ila ta amince da ita ta kai kayan agaji zuwa kudancin Gaza da aka yi wa ƙawanya saboda karuwar aikata laifuka da kuma kisan kiyashi da Isra'ila ke yi a kusa da wajen.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya shaida wa manema labarai cewa, hukumomin Isra'ila na ci gaba da takaita amfani da wasu hanyoyi zuwa hanyar da aka keɓe daga Karem Abu Salem - hanya daya tilo da ke tsallakawa daga Isra'ila zuwa kudancin Gaza - zuwa babbar hanyar Salah a-Din, babbar hanyar arewa da kudu.

"Hanyar da aka ce mu yi amfani da ita wajen shiga Kerem Shalom yanzu ba ta da tsaro a gare mu saboda karuwar aikata laifuka, don haka ba mu samu damar yin amfani da wannan hanyar ba."

#