Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, wanda yanzu ya shiga kwana na 363, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,638. Bugu da ƙari, sama da mutane 1,928 ne suka mutu a wani munanan hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon.
Alhamis, 3 ga Oktoban 2024
0606 GMT — Mayaƙan Houthi na Yemen sun yi iƙirarin kai hari a Tel Aviv
Mayaƙan Houthi na Yemen waɗanda ke samun goyon bayan Iran sun ce sun ƙaddamar da hari da jirgi mara matuƙi a Tel Aviv, ko da yake hukumomin Isra'ila ba su tabbatar da hakan ba.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta Houthi ta fitar, ta ce mayaƙanta sun "kai harin soji inda suka nufi yankin Jaffa (Tel Aviv) a yankin Falasɗinu da aka mamaye da wasu jirage marasa matuƙa na Jaffa".
"An cim ma burin kai harin cikin nasara domin kuwa jiragen marasa matuƙa sun isa inda aka harba su ba tare da maƙiya sun tunkare su ko harbo su ƙasa ba."
0625 GMT — Japan ta tura jiragen soji don kwashe 'yan ƙasarta daga Lebanon
Japan ta tura jiragen soji biyu zuwa Jordan da Girka domin shirin kwashe 'yan ƙasarta daga Lebanon, a cewar wasu rahotanni na kafofin watsa labaran ƙasar.
Rundunar Sojojin Sama ta Ƙasa ta tura jirage biyu samfurin C-2 daga Filin Jirgin Saman Miho Air da ke lardin Tottori na Japan, domin shirin kwashe 'yan ƙasar daga Lebanon, in ji kafar watsa labarai ta Kyodo News, wadda ta ambato Ma'aikatar Tsaron ƙasar.
Akwai 'yan ƙasar Japan 50 da ke zaune a Lebanon.
2331 GMT — Isra’ila ta kai harin bam a tsakiyar birnin Beirut da sanyin safiyar Alhamis, inda ta kashe akalla mutane shida, bayan da sojojinta masu mamaya suka ga mafi munin rana a gagarumin artabun da ba su taba irinsa ba a fagen daga tsakaninsu da kungiyar Hezbollah ta Lebanon a cikin shekara guda.
Shaidu sun ba da rahoton jin karar fashewar wani katon bam kuma wata majiyar tsaro ta ce Isra'ila ta kai hari kan wani gini da ke tsakiyar birnin Beirut a unguwar Bachoura da ke kusa da majalisar dokokin kasar, harin da Isra'ila ta kai a kusa da ofishin gwamnatin Lebanon.
Akalla mutum shida ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata, in ji jami'an kiwon lafiya na kasar Lebanon.
Wani hoto da ake yadawa a kafofin WhatsApp a kasar Lebanon ya nuna wani gini da ya lalace sosai tare da cin wuta a benensa na farko.
Har ila yau, sun kai harin makami mai linzami uku a yankin kudancin Dahiyeh, inda aka kashe shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah a makon da ya gabata, an kuma ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi kamar yadda jami'an tsaron kasar Labanon suka sanar.
Yankunan kudancin kasar sun fuskanci hare-hare sama da goma na Isra'ila a ranar Laraba.
Hukumar kula da bala'o'i ta kasar Lebanon ta fada a baya cewa mutane 1,928 Isra'ila ta kashe a kasar tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
2220 GMT — Isra'ila ta kashe wani Ba'amurke a Lebanon
Gwamnatin Amurka ta ce an kashe wani Ba’amurke dan asalin garin Dearborn a jihar Michigan, a kasar Labanon, inda abokin mutumin da makwabtansa suka ce an kashe shi ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama.
Kakakin Fadar White House ya ce "Muna matukar bakin ciki da rasuwar Kamel Ahmad Jawad, kuma muna mika ta'aziyyarmu ga 'yan uwansa da abokan arziki. Mutuwar tasa wata abar takaici ce, haka ma mutuwar fararen hula da dama a Lebanon."
Tun da farko dai, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, da aka tambaye shi game da rahotannin mutuwar wani Ba'amurke a Lebanon, ya ce: "A fahimtarmu ne cewa mazaunin kasar ne na dindindin bisa tsarin doka, ba wani Ba'amurke ba (wanda aka kashe a Lebanon) amma duk da haka muna mika ta'aziyyarmu ga 'yan uwa."