Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe gomman mutane a makarantar Al Fakhoura ta Gaza

1340 GMT — Isra'ila ta kashe gomman mutane a makarantar Al Fakhoura ta Gaza

Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu a wani hari da Isra’ila ta kai makarantar Al Fakhoura wadda ke dauke da dubban ‘yan gudun hijira a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta ruwaito.

Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu a wata sanarwa da ta fitar ta ce wannan ‘kisan kiyashin’ alama ce da ke nuna cewa yakin Isra’ila na son yi wa arewacin Gaza karkaf.

1300 GMT — Dakarun Al Quds Brigades sun yi ikitarin lalata tankokin yakin Isra'ila

Dakarun Al Quds Brigades na Falasdinawa sun ce sun lalata tankokin yakin Isra’ila biyu da kuma buldoza daya a Gaza, inda suka ce suna ci gaba da kai hari kan sauran kayayyakin soji na Isra’ila.

A wata sanarwa da Al Quds Brigades din ta fitar, ta bayyana cewa ta tayar da bam kan taron makiyanta a cikin dajin Kissufim da ke Zirin Gaza.

Al-Quds Brigades ce kungiya ta masu rike da makamai ta biyu mafi girma a Falasdinu bayan Hamas. / Hoto:Reuters

Haka kuma kungiyar ta ce dakarun nata sun kai hari kan motocin soji guda bakwai a Tal al Hawa da al Sabra da ke kudu maso yammacin birnin na Gaza.

1230 GMT — Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza

Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu da ke Gaza ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

“Wasu karin gawawwaki shida sun sake isowa Asibitin Al Aqsa sakamakon harin da masu mamaya suka kai gidan Aqtifan da ke Deir Al Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce ta kakkabo jirgin Isra’ila maras matuki da makami mai linzami a yankin Galilee Panhandle.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar da safe inda ta ce ta harba makamin nata da misalin karfe 1:45 agogon kasar, (23:45 agogon GMT).

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba. /Hoto:Reuters

Ta bayyana cewa ta hango lokacin da tarwatsatsun sassan jirgin ke fadawa a yankin Galilee Panhandle.

Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da sanarwa domin gasgatawa ko kuma karyata ikirarin na Hezbollah ba.

Sama da Falasdinawa 12,000 Isra’ila ta kashe zuwa yanzu, inda sama da 8,300 yara ne da mata, haka kuma ta raunata sama da 30,000.

#